Baibul a cikin shekara guda Agusta 20Ayuba 31:1-401. “Na yi alkawari da idanuna kada su dubi budurwa da muguwar sha’awa.2. Gama mene ne rabon mutum daga Allah a sama, gādonsa daga Maɗaukaki a sama?3. Ba masifa ba ne domin mugaye, hallaka kuma ga waɗanda suka yi ba daidai ba?4. Bai ga hanyoyina ba ne bai ƙirga kowace takawata ba?5. “In da na yi tafiya cikin rashin gaskiya ko kuma ƙafata ta yi sauri zuwa yin ƙarya,6. Bari Allah yă auna a kan ma’auni na gaskiya zai kuma san cewa ni marar laifi ne.7. In takawata ta kauce daga hanya, in zuciyata ta bi abin da idanuna ke so, ko kuma in hannuwana suna da laifi;8. bari waɗansu su ci abin da na shuka, kuma bari a tuge amfanin gonata.9. “In sha’awar mace ya shiga mini zuciya, ko kuma na laɓe a ƙofar maƙwabcina,10. sai matata ta niƙa hatsin wani kuma waɗansu maza su kwana da ita.11. Gama wannan zai zama abin kunya, zunubin da za a yi shari’a a kai.12. Wuta ce take ƙuna har ta hallakar; za tă cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.13. “In da na danne wa bayina maza da mata hakkinsu, sa’ad da suke da damuwa da ni,14. me zan yi lokacin da Allah ya tuhume ni? Me zan ce lokacin da ya tambaye ni?15. Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba? Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?16. “In na hana wa matalauta abin da suke so, ko kuma in sa idanun gwauruwa su yi nauyi don kuka,17. in na ajiye burodina don kaina kaɗai, ban kuwa ba wa marayu abinci sa’ad da suke jin yunwa,18. amma tun suna tasowa na lura da su, kamar yadda mahaifi zai lura da ɗa, kuma tun da aka haife ni ina lura da gwauruwa.19. In da na ga wani yana mutuwa don rashin sutura, ko wani mai bukata da ba shi da riga,20. kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba don na yi masa sutura da gashin tumakina,21. in na ɗaga hannuna don in cuci maraya, domin na san in na faɗa za a ji ni a wurin masu shari’a,22. bari hannuna yă guntule daga kafaɗata, bari yă tsinke daga inda aka haɗa shi.23. Gama ina jin tsoron hallaka daga Allah, kuma domin tsoron ɗaukakarsa ba zan iya yin waɗannan abubuwa ba.24. “In na dogara ga zinariya ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’25. in na yi fahariya don yawan dukiyata, arzikin da hannuwana suka samu.26. In na dubi rana cikin haskenta, ko kuma wata yana tafiyarsa,27. zuciyata ta jarrabtu gare su a ɓoye, hannuna kuma ya sumbace su.28. Waɗannan ma za su zama zunubin da za a shari’anta ke nan don zai zama na yi wa Allah na sama rashin aminci.29. “In na yi murna domin mugun abu ya faru da maƙiyina; ko kuma domin wahala ta same shi,30. ban bar bakina yă yi zunubi ta wurin la’anta shi ba,31. in mutanen gidana ba su taɓa cewa, ‘Wane ne bai ƙoshi da naman Ayuba ba?’32. Ba baƙon da ya taɓa kwana a titi, gama koyaushe ƙofata tana buɗe domin matafiya,33. in na ɓoye zunubina yadda mutane suke yi, ta wurin ɓoye laifina a cikin zuciyata,34. domin ina tsoron taron mutane kuma ina tsoron wulaƙancin da dangina za su yi mini, sai na yi shiru kuma ban fita waje ba.35. (“Kash, da ina da wanda zai ji ni! Na sa hannu ga abin da na faɗa don kāre kaina, bari Maɗaukaki yă amsa mini; bari mai tuhumata da laifi yă yi ƙarata a rubuce.36. Ba shakka sai in ɗora a kafaɗata, zan aza a kaina kamar rawani.37. Zan ba shi lissafin duk abin da na taɓa yi; zan zo gabansa kamar ɗan sarki.)38. “In ƙasata tana kuka da ni kunyoyinta duk sun cika da hawaye,39. in na kwashe amfaninta ban biya ba ko kuma na kashe masu ita,40. bari ƙaya ta fito a maimakon alkama ciyawa kuma a maimakon sha’ir.” Maganar Ayuba ta ƙare.Ayuba 32:1-221. Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin a ganinsa shi mai adalci ne.2. Amma Elihu ɗan Barakel mutumin Buz na iyalin Ram, ya ji haushi da Ayuba don yă nuna shi ne mai gaskiya ba Allah ba.3. Ya kuma ji haushin abokan nan guda uku, don sun kāsa amsa wa Ayuba ko da yake sun nuna Ayuba ne yake da laifi.4. Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka.5. Amma sa’ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da abin cewa, sai ya fusata.6. Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ce, “Ni ƙarami ne a shekaru, ku kuma kun girme ni; shi ya sa na ji tsoro na kāsa gaya muku abin da na sani.7. Na ɗauka ya kamata ‘shekaru su yi magana; ya kamata yawan shekaru su koyar da hikima.’8. Amma ruhun da yake cikin mutum, numfashin Maɗaukaki shi ne yake ba shi ganewa.9. Ba tsofaffi ne kaɗai suke da hikima ba, ba masu yawan shekaru ne suke gane abin da yake daidai ba.10. “Saboda haka nake ce muku, ku saurare ni; ni ma zan gaya muku abin da na sani.11. Na jira sa’ad da kuke magana, na ji muhawwararku lokacin da kuke neman abin da za ku faɗa,12. na saurare ku da kyau. Amma ba waninku da ya nuna Ayuba yana da laifi; ba ko ɗayanku da ya amsa muhawwararsa.13. Kada ku ce, ‘Mun sami hikima; Allah ne kaɗai yake da ikon yin nasara da shi ba mutum ba.’14. Amma ba da ni Ayuba ya yi gardama ba kuma ba zan amsa masa da irin amsarku ba.15. “Mamaki ya kama su kuma ba su da abin cewa; kalmomi sun kāsa musu.16. Dole ne in jira yanzu da suka yi shiru, yanzu da suke tsaye a wurin ba su da amsa.17. Ni ma zan faɗi nawa; ni ma zan faɗi abin da na sani.18. Gama ina cike da magana, kuma ruhun da yake cikina yana iza ni;19. a ciki ina kamar ruwan inabi wanda aka rufe a cikin kwalaba, kamar sabuwar salkar ruwan inabi mai shirin fashewa.20. Dole in yi magana in sami lafiya; dole in buɗe baki in ba da amsa.21. Ba zan nuna wa wani sonkai ba, ko kuma in yi wa wani daɗin baki ba;22. gama da a ce na iya daɗin baki, da wanda ya yi ni ya ɗauke ni daga nan tuntuni.Zabura 98:1-31. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto.2. Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.3. Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu.Karin Magana 23:17-1817. Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi, amma kullum tsoron Ubangiji za ka yi kishi.18. Tabbatacce akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.1 Korintiyawa 2:1-161. Da na zo wurinku ’yan’uwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba.2. Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye.3. Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai.4. Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu,5. domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.6. Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba.7. A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai.8. Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba.9. Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ba idon da ya taɓa gani, ba kunnen da ya taɓa ji, ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”10. Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa. Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah.11. Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah.12. Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake.13. Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya.14. Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu.15. Mutumin ruhaniya yakan gwada dukan abubuwa, amma shi kansa ba ya ƙarƙashin shari’ar mutum.16. “Wa ya taɓa sanin hankalin Ubangiji, har da zai koya masa?” Amma muna da tunani iri na Kiristi ne. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.