Baibul a cikin shekara guda Agusta 21Ayuba 33:1-331. “Amma yanzu, Ayuba, ka saurari abin da zan ce; ka sa hankali ga kowane abin da zan faɗa.2. Zan yi magana; kalmomina suna dab da fitowa daga bakina.3. Abin da zan faɗa gaskiya ne daga cikin zuciyata; bakina zai faɗi gaskiyar abin da na sani.4. Ruhun Allah ne ya yi ni; numfashin Maɗaukaki ya ba ni rai.5. Ka amsa mini in za ka iya; ka yi shirin fuskanta ta.6. Ni kamar ka nake a gaban Allah; ni ma daga ƙasa aka yi ni.7. Kada ka ji tsorona, ba abin da zai fi ƙarfinka.8. “Amma ka faɗa na ji, na ji daidai abin da ka faɗa,9. ‘ni mai tsarki ne marar zunubi; ina da tsabta kuma ba ni da laifi.10. Duk da haka Allah ya same ni da laifi; ya ɗauke ni maƙiyinsa,11. ya daure ƙafafuna da sarƙa; yana tsaron duk inda na bi.’12. “Amma na gaya maka, a nan ba ka yi daidai ba, gama Allah ya fi mutum girma.13. Don me ka yi masa gunaguni cewa ba ya amsa tambayoyin mutum?14. Gama Allah yana magana, yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya ko da yake ba lalle mutum yă lura ba.15. A cikin mafarki, cikin wahayi da dare, sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane lokacin da suke cikin barci kan gadajensu,16. mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu yă razana su da gargaɗinsa,17. don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba a kuma hana su daga girman kai,18. don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami, a kāre su daga hallaka ta wurin takobi.19. “Ko kuma mutum yă sha horo ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa,20. yadda zai ji ƙyamar abinci, har yă ƙi son abinci mafi daɗi.21. Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito.22. Ransa yana matsawa kusa da rami, ransa kuma kusa da ’yan aikan mutuwa.23. Duk da haka, in akwai mala’ika a gefensa kamar matsakanci, ɗaya daga cikin dubu, da zai gaya wa mutum abin da yake daidai gare shi,24. yă yi masa alheri yă ce, ‘Kada ka bari yă fāɗa cikin rami, na samu fansa dominsa.’25. Sa’an nan fatar jikinsa za tă zama sabuwa kamar ta jariri; za tă zama kamar lokacin da yake matashi.26. Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa, yana ganin fuskar Allah yana kuma yin sowa don murna; Allah ya mayar da shi ya zama mai adalci.27. Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce, ‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai, amma ban samu abin da ya kamata in samu ba.28. Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami, kuma zan rayu in ji daɗin hasken.’29. “Allah ya yi wa mutum duk waɗannan, sau biyu, har ma sau uku.30. Ya juyo da ransa daga fāɗawa cikin rami, don hasken rai ya haskaka a kansa.31. “Ka sa hankali da kyau, Ayuba, ka saurare ni; ka yi shiru zan yi magana.32. In kana da abin da za ka ce, ka amsa mini; yi magana, domin ina so in ’yantar da kai.33. Amma in ba haka ba, sai ka saurare ni; yi shiru, zan kuma koya maka hikima.”Ayuba 34:1-371. Sa’an nan Elihu ya ce,2. “Ku ji maganata, ku masu hikima; ku saurare ni, ku masu ilimi.3. Gama kunne yana rarrabe magana kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci.4. Bari mu zaɓi abin da yake daidai, bari mu koyi abin da yake mai kyau tare.5. “Ayuba ya ce, ‘Ba ni da laifi, amma Allah ya hana mini hakkina.6. Ko da yake ina da gaskiya, an ɗauke ni maƙaryaci; ko da yake ba ni da laifi, kibiyoyinsa sun ji mini ciwo wanda ba ya warkewa.’7. Wane mutum ne kamar Ayuba, wanda yake shan ba’a kamar ruwa?8. Yana abokantaka da masu aikata mugunta; yana cuɗanya da mugaye.9. Gama ya ce, ‘Ba ribar da mutum zai samu lokacin da yake ƙoƙari yă faranta wa Allah zuciya.’10. “Saboda haka ku saurare ni, ku masu ganewa. Ko kaɗan Allah ba ya mugunta, Maɗaukaki ba ya kuskure.11. Yana biyan mutum bisa ga abin da ya yi; yana kawo masa abin da ayyukansa suka jawo.12. Ba zai yiwu Allah yă yi ba daidai ba, Maɗaukaki ba zai yi shari’a marar gaskiya ba.13. Wane ne ya ba shi iko yă lura da duniya? Wane ne ya ba shi iko kan dukan duniya?14. In nufinsa ne ya kuma janye ruhunsa da numfashinsa,15. ’yan adam duka za su hallaka tare, mutum kuma zai koma ƙasa.16. “In kana da ganewa sai ka saurari wannan; ka saurari abin da zan ce.17. Maƙiyin gaskiya zai iya yin mulki? Za ka iya ba mai gaskiya, Maɗaukaki laifi?18. Ba shi ne ya ce wa sarakuna, ‘Ba ku da amfani ba,’ ya ce wa manya ‘Ku mugaye ne,’19. wanda ba ya nuna sonkai ga ’ya’yan sarki kuma ba ya goyon bayan masu arziki a kan matalauta, gama dukansu shi ya yi su da hannuwansa.20. Suna mutuwa nan take, a cikin tsakiyar dare; an girgiza mutanen amma sun wuce; an taɓa manya amma ba da hannun mutum ba.21. “Idanunsa suna kan al’amuran mutane; yana ganin tafiyarsu duka.22. Babu wuri mai duhu, babu inuwa mai duhu, inda masu aikata mugunta za su ɓoye.23. Allah ba ya bukata yă ci gaba da bincike mutane, har da za su zo gabansa don yă shari’anta su.24. Ba tare da tambaya ba yana ragargaza masu iko, yă kuma sa waɗansu a wurinsu.25. Gama yana sane da abubuwan da suke yi, yana hamɓarar da su da dare a kuma ragargaza su.26. Yana ba su horo, don muguntarsu, inda kowa zai gan su,27. domin sun juya daga binsa, kuma ba su kula da hanyoyinsa ba.28. Sun sa kukan matalauta ya kai wurinsa yadda ya kai ga jin kukan masu bukata.29. Amma in ya yi shiru, wa zai ba shi laifi? In ya ɓoye fuskarsa, wa zai gan shi? Duk da haka shi yake da iko kan mutum da al’umma duka,30. yana hana wanda bai san Allah ba yă yi mulki, ya hana shi sa wa mutane tarko.31. “A ce mutum ya ce wa Allah, ‘Na yi laifi, amma ba zan sāke saɓa wa wani ba.32. Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba; in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’33. Ya kamata Allah yă yi maka bisa ga abin da ka ce ne, sa’ad da ka ƙi ka tuba? Dole kai ka zaɓa, ba ni ba; yanzu ka gaya mini abin da ka sani.34. “Mutane masu ganewa za su ce, masu hikima waɗanda suka ji ni za su ce mini,35. ‘Ayuba ya yi magana cikin rashin sani; maganganunsa na marar hikima ne.’36. Kash, da za a gwada Ayuba har ƙarshe, domin yana ba da amsa kamar mugun mutum.37. Ya ƙara tawaye a kan zunubansa; ya tafa hannuwansa na reni a cikinmu ya kuma ƙara yawan maganganunsa ga Allah.”Zabura 98:4-94. Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya, ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;5. ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya, da garaya da ƙarar rerawa,6. tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago, ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.7. Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa, duniya da kuma kome da yake cikinta.8. Bari koguna su tafa hannuwansu, bari duwatsu su rera tare don farin ciki;9. bari su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa domin yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci mutane kuma cikin gaskiya.Karin Magana 23:19-2119. Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima, ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai.20. Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa ko masu haɗama kansu da abinci,21. gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.1 Korintiyawa 3:1-231. ’Yan’uwa, ban iya yi muku magana kamar masu ruhaniya ba, sai dai kamar masu halin mutuntaka, jarirai cikin bin Kiristi kawai.2. Na ba ku madara ba abinci mai tauri ba, domin ba ku balaga ba a lokacin. Kai, har yanzu ma, ba ku balaga ba.3. Har yanzu kuna rayuwa bisa ga halin mutuntaka. Da yake akwai kishi da faɗace-faɗace a cikinku, ba rayuwa irin ta halin mutuntaka ke nan kuke yi ba? Kuma ba rayuwa irin ta mutane ce kawai kuke yi ba?4. Gama sa’ad da wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afollos ne,” ba rayuwa irin ta mutane ke nan kuke yi ba?5. Shin, wane ne Afollos? Wane ne kuma Bulus? Ai, bayi ne kawai waɗanda ta wurinsu kuka gaskata, kamar yadda Ubangiji ya ba kowannensu aikinsa.6. Ni na shuka iri, Afollos kuma ya yi banruwa, amma Allah ne ya sa irin ya yi girma.7. Don haka, da wanda ya yi shuki, da wanda ya yi banruwa, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, mai sa abubuwa su yi girma.8. Mutumin da ya yi shuki, da mutumin da ya yi banruwa nufinsu ɗaya ne, kuma kowannensu zai sami lada gwargwadon aikinsa.9. Gama mu abokan aiki ne na Allah; ku kuwa gonar ce ta Allah, ginin Allah kuma.10. Ta wurin alherin da Allah ya ba ni, na kafa tushen gini kamar ƙwararren magini, wani kuma dabam yana gini a kai. Amma kowa yă lura da yadda yake gini.11. Gama babu wanda zai iya kafa wani tushen gini dabam da wanda aka riga aka kafa, wanda yake Yesu Kiristi.12. In wani ya yi gini a kan tushen ginin nan da zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja, itace, ciyawa ko kara,13. aikin zai bayyana kansa, domin za a nuna shi a sarari a Ranar. Wuta ce za tă bayyana aikin, wutar kuwa za tă gwada ingancin aikin kowa.14. In abin da kowane mutum ya gina ya tsaya, zai sami lada.15. In ya ƙone, zai yi hasara, amma zai sami ceto, sai dai kamar wanda ya bi ta tsakiyar wuta ne.16. Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku?17. Duk wanda ya ɓata haikalin Allah, Allah zai ɓata shi, don haikalin Allah mai tsarki ne, ku ne kuwa haikalin nan.18. Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima.19. Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”;20. kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.”21. Saboda haka, kada wani yă yi taƙama da mutum! Gama kome naku ne,22. ko Bulus ko Afollos ko Kefas ko duniya ko rai ko mutuwa ko abubuwa na yanzu ko na nan gaba, ai, duka naku ne,23. ku kuwa na Kiristi ne, Kiristi kuma na Allah ne. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.