Baibul a cikin shekara guda Agusta 22Ayuba 35:1-161. Sai Elihu ya ce,2. “Ko kana tsammani wannan gaskiya ne? Kana cewa, ‘Ni mai adalci ne a gaban Allah.’3. Duk da haka kana tambayarsa cewa, ‘Wace riba nake da ita, kuma mene ne zan samu ta wurin ƙin yin zunubi?’4. “Zan so in ba ka amsa kai tare da abokanka.5. Ku ɗaga kai ku dubi sama ku gani; ku dubi gizagizai a samanku.6. In kun yi zunubi ta yaya wannan zai shafi Allah? In zunubanku sun yi yawa, me wannan zai yi masa?7. In kuna da adalci, me kuka ba shi, ko kuma me ya karɓa daga hannunku?8. Muguntarku takan shafi mutum kamar ku ne kaɗai, adalcinku kuma yakan shafi ’yan adam ne kaɗai.9. “Mutane suna kuka don yawan zalunci; suna roƙo don taimako daga hannu mai ƙarfi.10. Amma ba wanda ya ce, ‘Ina Allah wanda ya halicce ni, mai ba da waƙoƙi cikin dare,11. wanda ya fi koya mana fiye da dabbobin duniya ya kuma sa muka fi tsuntsayen cikin iska hikima.’12. Ba ya amsawa lokacin da mutane suka yi kira don taimako domin girman kan mugaye.13. Lalle Allah ba ya sauraron roƙonsu na wofi; Maɗaukaki ba ya kula da roƙonsu.14. Ta yaya zai saurara sosai ko zai saurara lokacin da kake cewa ba ka ganinsa, cewa ka kawo ƙara a wurinsa kuma dole ka jira shi.15. Kuma ka ce, ba ya ba da horo cikin fushinsa ko kaɗan ba ya kula da mugunta.16. Saboda haka Ayuba ya buɗe baki yana magana barkatai; yana ta yawan magana ba tare da sani ba.”Ayuba 36:1-331. Elihu ya ci gaba,2. “Ka ɗan ƙara haƙuri da ni kaɗan, zan kuma nuna maka cewa akwai sauran abubuwan da zan faɗa a madadin Allah.3. Daga nesa na sami sanina; zan nuna cewa Mahaliccina shi mai gaskiya ne.4. Abin da zan gaya maka ba ƙarya ba ne; mai cikakken sani yana tare da kai.5. “Allah mai iko ne, amma ba ya rena mutane; shi mai girma ne cikin manufarsa.6. Ba ya barin mugaye da rai sai dai yana ba waɗanda ake tsanantawa hakkinsu.7. Ba ya fasa duban masu adalci; yana sa su tare da sarakuna yana ɗaukaka su har abada.8. Amma in mutane suna daure da sarƙoƙi, ƙunci kuma ya daure su,9. yana gaya musu abin da suka yi, cewa sun yi zunubi da girman kai.10. Yana sa su saurari gyara yă kuma umarce su su tuba daga muguntarsu.11. In sun yi biyayya suka bauta masa, za su yi rayuwa dukan kwanakinsu cikin wadata shekarunsu kuma cikin kwanciyar zuciya.12. Amma in ba su saurara ba, za su hallaka da takobi kuma za su mutu ba ilimi.13. “Waɗanda ba su da Allah a zuciyarsu su ne suke riƙe fushi; ko sa’ad da ya ba su horo, ba su neman taimakonsa.14. Suna mutuwa tun suna matasa, cikin ƙazamar rayuwar karuwanci.15. Amma yana kuɓutar da masu wahala; yana magana da su cikin wahalarsu.16. “Yana so yă rinjaye ka daga haƙoran ƙunci, zuwa wuri mai sauƙi inda ba matsi zuwa teburinka cike da abincin da kake so.17. Amma yanzu an cika ka da hukuncin da ya kamata a yi wa mugaye; shari’a da kuma gaskiya sun kama ka.18. Ka yi hankali kada wani yă ruɗe ka da arziki; kada ka bar toshiya ta sa ka juya.19. Dukiyarka ko dukan yawan ƙoƙarinka sun isa su riƙe ka su hana ka shan ƙunci?20. Kada ka yi marmari dare yă yi, don a fitar da mutane daga gidajensu.21. Ka kula kada ka juya ga mugunta, abin da ka fi so fiye da wahala.22. “An ɗaukaka Allah cikin ikonsa. Wane ne malami kamar sa?23. Wane ne ya nuna masa hanyar da zai bi, ko kuma wane ne ya ce masa, ‘Ba ka yi daidai ba?’24. Ka tuna ka ɗaukaka aikinsa, waɗanda mutane suka yaba a cikin waƙa.25. Dukan ’yan adam sun gani; mutane sun hanga daga nesa.26. Allah mai girma ne, ya wuce ganewarmu! Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.27. “Yana sa ruwa yă zama tururi yă zubo daga sama.28. Gizagizai suna zubo da raɓarsu kuma ruwan sama yana zubowa ’yan adam a wadace.29. Wane ne zai iya gane yadda ya shimfiɗa gizagizai yadda yake tsawa daga wurin zamansa?30. Dubi yadda ya baza walƙiyarsa kewaye da shi, tana haskaka zurfin teku.31. Haka yake mulkin al’ummai yana kuma tanada abinci a wadace.32. Yana cika hannuwansa da walƙiya kuma yana ba ta umarni tă fāɗi a inda ya yi nufi.33. Tsawarsa tana nuna cewa babbar iska da ruwa suna zuwa; ko shanu sun san da zuwansa.Zabura 99:1-91. Ubangiji yana mulki, bari al’ummai su yi rawan jiki; yana zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, bari duniya ta girgiza.2. Ubangiji mai girma yana a Sihiyona; an ɗaukaka shi a bisa dukan al’ummai.3. Bari mu yabi girmanka da sunanka mai banrazana, shi mai tsarki ne.4. Sarki mai iko ne, yana ƙaunar adalci ka kafa gaskiya; a cikin Yaƙub ka yi abin da yake mai adalci da kuma daidai.5. Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu ku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa; shi mai tsarki ne.6. Musa da Haruna suna cikin firistocinsa, Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa; sun kira ga Ubangiji ya kuwa amsa musu.7. Ya yi magana da su daga ginshiƙin girgije; ya kiyaye farillansa da ƙa’idodin da ya ba su.8. Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa musu; ka kasance wa Isra’ila Allah mai gafartawa, ko da yake ka hukunta ayyukansu marasa kyau.9. Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu ku kuma yi sujada a dutsensa mai tsarki, gama Ubangiji Allahnmu mai tsarki ne.Karin Magana 23:22-2522. Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai, kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.23. Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita; ka nemi hikima, horo da fahimi.24. Mahaifin adali yana da farin ciki sosai; duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.25. Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna; bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki!1 Korintiyawa 4:1-211. Saboda haka, ya kamata mutane su ɗauke mu a matsayin bayin Kiristi, da kuma a matsayin waɗanda aka ba su amanar asirin abubuwan Allah.2. Yanzu fa, ana bukatar waɗanda aka ba su riƙon amana, dole su zama masu aminci.3. Ƙaramin abu ne a gare ni a ce ku ne za ku gwada ni, ko kuwa a gwada ni a wata kotun mutane, ai, ko ni kaina ba na yanka wa kaina hukunci.4. Lamirina bai ba ni laifi ba, sai dai wannan bai mai da ni marar laifi ba. Ubangiji ne mai hukunta ni.5. Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.6. To, fa ’yan’uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afollos saboda ku, don ku yi koyi da mu a kan abin da ake nufi da cewa, “Kada ku zarce abin da yake a rubuce.” Ta haka, ba za ku yi taƙama da wani mutum fiye da wani ba.7. Wa ya ce ka fi sauran mutane? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? In kuma karɓa ka yi, me ya sa kake taƙama kamar ba karɓa ba ne ka yi?8. Kun riga kun sami duk abin da kuke nema! Kun riga kun yi arziki! Kun zama sarakuna, kun kuma zama haka ɗin ba tare da mu ba! Da a ce kun riga kun zama sarakuna mana da sai mu zama sarakuna tare da ku!9. Gama a ganina fa, Allah ya baje mu manzanni a ƙarshen jerin gwanon, a matsayin mutanen da aka hukunta ga mutuwa a filin wasanni. Mun zama abin kallo ga dukan duniya, ga mala’iku da kuma mutane.10. Mun zama masu wauta saboda Kiristi, ku kuwa kuna da hikima sosai a cikin Kiristi! Ba mu da ƙarfi, amma ku kuna da ƙarfi! Ana girmama ku, mu kuwa ana ƙasƙantar da mu!11. Har yă zuwa wannan sa’a, yunwa da ƙishirwa muke ciki, muna sanye da tsummoki, ana wulaƙanta mu, ba mu kuma da gida.12. Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka la’anta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre;13. in aka ɓata mana suna, mukan mayar da alheri. Har yă zuwa wannan lokaci, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.14. Ba don in kunyata ku ba ne na rubuta wannan, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa ku ’ya’yana ne, ƙaunatattu.15. Ko da kuna da iyayen riƙo dubu goma cikin Kiristi, ba ku da ubanni da yawa, gama a cikin Kiristi Yesu, na zama mahaifi a gare ku, ta wurin bishara.16. Saboda haka, ina roƙonku ku yi koyi da ni.17. Saboda wannan dalili ina aika muku Timoti, ɗana, wanda nake ƙauna, mai aminci kuma a cikin Ubangiji. Zai tunashe ku game da yadda za ku bi Kiristi Yesu da kuma yadda ya yi daidai da yadda nake koyarwa a ko’ina, a kowace ikkilisiya.18. Waɗansunku suna tsammani ba zan zo wurinku ba har suna ɗagankai.19. Amma in Ubangiji ya yarda zan zo wurinku ba da daɗewa ba. Sa’an nan zan bincike ko masu wannan yawan ɗagan kan nan suna da wani iko.20. Gama mulkin Allah ba cika baki ba ne, sai dai ga iko.21. Wanne kuka fi so in na zo? Kuna so in tsananta muku ko in zama mai hankali da kuma sauƙinkai? Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.