Baibul a cikin shekara guda Agusta 23Ayuba 37:1-241. “Wannan ya sa gabana ya fāɗi, zuciyata ta yi tsalle.2. Ka saurara! Ka saurari rurin muryarsa, tsawar da take fita daga bakinsa.3. Ya saki walƙiyarsa, a ƙarƙashin dukan sammai ya kuma aika ta ko’ina a cikin duniya.4. Bayan wannan sai ƙarar rurinsa ta biyo; Ya tsawata da muryarsa mai girma. Sa’ad da ya sāke yin tsawa ba ya rage wani abu.5. Muryar Allah tana tsawatawa a hanyoyi masu ban al’ajabi; yana yin manyan abubuwa waɗanda sun wuce ganewarmu.6. Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’ ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’7. Domin dukan mutanen da ya halitta za su san aikinsa, ya hana kowane mutum yin wahalar aiki.8. Dabbobi sun ɓoye; sun zauna cikin kogunansu.9. Guguwa tana fitowa daga inda take, sanyi kuma daga iska mai sanyi.10. Da numfashinsa Allah yana samar da ƙanƙara sai manyan ruwaye su zama ƙanƙara.11. Yana cika gizagizai da lema; yana baza walƙiyarsa ta cikinsu.12. Bisa ga bishewarsa suke juyawa a kan fuskar duniya, suna yin dukan abin da ya umarce su su yi.13. Yana aiko da ruwa domin horon mutane, ko kuma don yă jiƙa duniya yă kuma nuna ƙaunarsa.14. “Ka saurari wannan Ayuba; ka tsaya ka dubi abubuwan al’ajabi na Allah.15. Ko ka san yadda Allah yake iko da gizagizai ya kuma sa walƙiyarsa ta haskaka?16. Ko ka san yadda gizagizai suke tsayawa cik a sararin sama, waɗannan abubuwa al’ajabi na mai cikakken sani.17. Kai mai sa kaya don ka ji ɗumi lokacin da iska mai sanyi take hurawa,18. ko za ka iya shimfiɗa sararin sama tare da shi da ƙarfi kamar madubi?19. “Gaya mana abin da ya kamata mu ce masa; ba za mu iya kawo ƙara ba domin duhunmu.20. Ko za a gaya masa cewa ina so in yi magana? Ko wani zai nemi a haɗiye shi?21. Yanzu ba wanda zai iya kallon rana, yadda take da haske a sararin sama bayan iska ta share ta.22. Yana fitowa daga arewa da haske na zinariya, Allah yana zuwa da ɗaukaka mai ban al’ajabi.23. Maɗaukaki ya fi ƙarfin ganewarmu, shi babban mai iko ne, mai gaskiya da babban adalci, ba ya cutar mutum.24. Saboda haka, mutane suke girmama shi, ko bai kula da waɗanda suke gani su masu hikima ba ne?”Ayuba 38:1-411. Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce,2. “Wane ne wannan da yake ɓata mini shawarata da surutan wofi?3. Ka sha ɗamara kamar namiji; zan yi maka tambaya, za ka kuwa amsa mini.4. “Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya? Gaya mini, in ka sani.5. Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani! Wane ne ya ja layin aunawa a kanta?6. A kan me aka kafa tushenta, ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta,7. yayinda taurarin safe suke waƙa tare dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki.8. “Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi, lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki.9. Lokacin da na yi wa gizagizai riga na kuma naɗe su a cikin duhu sosai,10. sa’ad da na yi masa iyaka na sa masa ƙofofi da wurin kullewa.11. Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai, ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya?12. “Ko ka taɓa ba safiya umarni ko kuma ka sa asuba ta fito,13. don ta kama gefen duniya ta kakkaɓe mugaye daga cikinta?14. Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi; ta fito a fili kamar riga.15. An hana mugaye haskensu, hannun da suka ɗaga an karya shi.16. “Ko ka taɓa tafiya zuwa maɓulɓulan teku, ko kuma ka taɓa zuwa cikin zurfin lungun teku?17. Ko an taɓa nuna maka ƙofar mutuwa? Ko ka taɓa ganin ƙofar inuwar duhun mutuwa?18. Ko ka gane fāɗin duniya? Gaya mini, in ka san wannan duka.19. “Ina ne hanyar zuwa gidan haske? Kuma a ina duhu yake zama?20. Ko za ka iya kai su wurarensu? Ka san hanyar zuwa wurin da suke zama?21. Ba shakka ka sani, gama an riga an haife ka a lokacin! Ka yi shekaru da yawa kana rayuwa.22. “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara23. waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala, domin kwanakin yaƙi da faɗa?24. Ina ne hanyar zuwa wurin da ake samun walƙiya, ko kuma inda daga nan ne ake watsa iskar gabas zuwa ko’ina cikin duniya?25. Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa, da kuma hanyar walƙiyar tsawa26. don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin jeji inda ba mai zama ciki27. don a ƙosar da wurin da ya bushe a sa ciyawa ta tsiro a can?28. Ruwan sama yana da mahaifi? Wa ya zama mahaifin raɓa?29. Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara? Wane ne ya haifi jaura daga sammai30. lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse, lokacin da saman ruwa ya daskare?31. “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta? Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?32. Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje?33. Ka san dokokin sammai? Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya?34. “Za ka iya tsawata wa gizagizai ka kuma rufe kanka da ambaliyar ruwa?35. Kai ne kake aika walƙiya da tsawa zuwa inda suke zuwa? Ko suna zuwa wurinka su ce, ‘Ga mu nan mun zo?’36. Wane ne yake cika zuciya da hikima ko kuma yake ba zuciya ganewa?37. Wane ne yake da hikimar iya ƙirga gizagizai? Wane ne zai iya karkato bakunan tulunan sammai38. sa’ad da ƙura ta yi yawa ta daskare a wuri ɗaya?39. “Za ka iya farauto wa zakanya nama, ka kuma kawar wa zakoki yunwarsu.40. Lokacin da suka kwanta cikin kogunansu, ko kuma lokacin da suke a wurin ɓuyansu?41. Wane ne yake ba hankaka abinci lokacin da ’ya’yansa suke kuka ga Allah, kuma suna yawo don rashin abinci?Zabura 100:1-51. Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.2. Yi wa Ubangiji sujada da murna; ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.3. Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah. Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne; mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.4. Ku shiga ƙofofinsa da godiya filayen gidansa kuma da yabo; ku gode masa ku kuma yabi sunansa.5. Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada; amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.Karin Magana 23:26-2826. Ɗana, ka ba ni zuciyarka bari kuma idanunka su kiyaye hanyoyina,27. gama karuwa rami ne mai zurfi mace marar aminci matsattsiyar rijiya ce.28. Kamar ’yan fashi, takan kwanta tana jira tana kuma ninka rashin aminci a cikin maza.1 Korintiyawa 5:1-131. Ana ba da labari cewa ana lalata a cikinku, irin da ba a ma samu a cikin masu bautar gumaka. Har mutum yana kwana da matar mahaifinsa.2. Har ya zama muku abin taƙama! Ashe, bai kamata ku cika da baƙin ciki ku kuma daina zumunci da mutumin da yake aikata wannan ba?3. Ko da yake ba na nan tare da ku cikin jiki, ina tare da ku a cikin ruhu. Na riga na yanke wa wanda ya aikata wannan hukunci, kamar dai ina tare da ku.4. Saboda haka sa’ad da kun taru ikon Ubangijinmu Yesu kuma yana nan, ni ma ina tare da ku.5. Ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don a hallaka halin nan na mutuntaka, ruhunsa kuma yă sami ceto a ranar da Ubangiji zai dawo.6. Ku daina taƙama. Ba ku san cewa ɗan ƙanƙanin yisti ne yakan sa dukan curin burodi yă kumbura ba?7. Ku kawar da tsohon yisti don ku zama kamar sabon curi da aka yi babu yisti yadda dai kuke. Gama an miƙa Kiristi Ɗan Ragon Bikin Ƙetarewarmu.8. Saboda haka, sai mu kiyaye Bikin ba da burodi mai tsohon yisti ba, ba kuma da yisti na ƙeta da mugunta ba, sai dai da burodi marar yisti na sahihanci da na gaskiya.9. Na rubuta muku cikin wasiƙata, kada ku yi haɗa kai da masu aikin lalata.10. Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya.11. Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum.12. Me zai kai yin hukunci ga waɗanda ba ’yan ikkilisiya ba. Ai, waɗanda suke ’yan ikkilisiya ne za ku hukunta.13. Allah zai hukunta waɗanda ba namu ba. “Ku yi waje da irin mugun mutumin nan daga cikinku.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.