Baibul a cikin shekara guda Agusta 24Ayuba 39:1-301. “Ka san lokacin da awakin kan dutse suke haihuwa? Ko ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?2. Kana ƙirga watanni nawa suke yi kafin su haihu? Ka san lokacin da suke haihuwa?3. Suna kwanciya su haifi ’ya’yansu; naƙudarsu ta ƙare bayan sun haihu.4. ’Ya’yansu suna girma kuma suna girma cikin ƙarfi a jeji; sukan tafi ba su dawowa.5. “Wane ne yake sakin jakin dawa yă bar shi? Wane ne yake kunce igiyoyinsu?6. Na sa jeji yă zama gidansa ƙasar gishiri kuma ta zama wurin zamansa.7. Yana dariyar hargitsin da yake faruwa a cikin gari; ba ya jin tsawar mai tuƙa shi.8. Yana kiwo a kan tuddai don abincinsa yana neman kowane ɗanyen abu mai ruwan ciyawa.9. “Ko ɓauna zai yarda yă zauna a wurin sa wa dabbobi abinci? Zai tsaya a ɗakin dabbobinka da dare?10. Ko za ka iya daure shi da igiya a kwarin kunya? Zai yi maka buɗar gonarka?11. Ko za ka dogara da shi don yawan ƙarfinsa? Za ka bar masa nauyin aikinka?12. Ko za ka amince da shi yă kawo maka hatsinka gida yă tattara shi a masussuka?13. “Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki amma ba za su gwada kansu da fikafikan da na shamuwa ba.14. Tana sa ƙwai nata a ƙasa kuma ta bar su su yi ɗumi a cikin ƙasa,15. ba tă damu ko za a taka su a fasa su, ko waɗansu manyan dabbobi za su tattake su.16. Tana tsananta wa ’ya’yanta kamar ba nata ba ba tă damu da wahalar da ta sha ba.17. Gama Allah bai ba ta hikima ba ko kuma iya fahimta.18. Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu tana yi wa doki da mai hawansa dariya.19. “Ko kai ne kake ba doki ƙarfinsa kai kake rufe wuyansa da geza mai yawa?20. Ko kai kake sa shi yă yi tsalle kamar fāra, ba ya jin tsoro sai dai a ji tsoronsa.21. Yana takawa da ƙarfi yana jin daɗin ƙarfinsa yana shiga filin yaƙi gabagadi.22. Yana yi wa tsoro dariya ba ya jin tsoron kome; ba ya guje wa takobi.23. Kwari a baka yana lilo a gabansa kibiya da māshi suna wuce kansa.24. Yana kartar ƙasa da ƙarfi; ba ya iya tsayawa tsab sa’ad da ya ji busar ƙaho.25. Da jin ƙarar ƙaho sai ya ce, ‘Yauwa!’ Ya ji ƙanshin yaƙi daga nesa, da ihun shugabannin yaƙi.26. “Ko ta wurin hikimarka ce shirwa take firiya take kuma baza fikafikanta zuwa kudu?27. Ko da umarninka ne shaho yake firiya ya kuma yi sheƙarsa a can sama?28. Yana zama a kan dutse yă zauna a wurin da dare; cikin duwatsu ne wurin zamansa.29. Daga can yake neman abincinsa; idanunsa suna gani daga nesa.30. ’Ya’yansa suna shan jini, inda akwai waɗanda aka kashe nan za a same shi.”Ayuba 40:1-241. Ubangiji ya ce wa Ayuba,2. “Mai neman sa wa wani laifi zai iya ja da Maɗaukaki? Bari mai tuhumar Allah yă amsa masa.”3. Sai Ayuba ya amsa wa Ubangiji,4. “Ai, ni ba a bakin kome nake ba ne, ta yaya zan iya amsa maka? Na rufe bakina da hannuna.5. Na yi magana sau ɗaya amma ba ni da amsa, sau biyu, amma ba zan ƙara cewa kome ba.”6. Sa’an nan Ubangiji ya yi wa Ayuba magana ta cikin guguwa,7. “Ka tashi tsaye ka tsaya da ƙarfi kamar namiji; zan yi maka tambaya kuma za ka amsa mini.8. “Ko za ka ƙi yarda da shari’ata? Za ka ba ni laifi don ka nuna kai marar laifi ne?9. Ko hannunka irin na Allah ne, kuma ko muryarka za tă iya tsawa kamar ta Allah?10. Sai ka yi wa kanka ado da ɗaukaka da girma, ka yafa daraja da muƙami.11. Ka saki fushinka, ka dubi dukan wani mai girman kai ka wulaƙanta shi.12. Ka dubi duk wani mai girman kai ka ƙasƙantar da shi, ka tattake mugaye a inda ka tsaya.13. Ka bizne su duka tare ka rufe fuskokinsu a cikin kabari.14. Sa’an nan ni kaina zan shaida maka cewa hannun damanka zai iya cetonka.15. “Dubi dorina, wadda na halicce ku tare kuma ciyawa take ci kamar sa.16. Ga shi ƙarfinta yana a ƙugunta ikonta yana cikin tsokar cikinta.17. Wutsiyarta tana da ƙarfi kamar itacen al’ul; jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe a wuri ɗaya.18. Ƙasusuwanta bututun tagulla ne, haƙarƙarinta kamar sandunan ƙarfe.19. Tana ta farko cikin ayyukan Allah, Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkarar ta da takobi.20. Tuddai su suke tanada mata abinci a inda duk namun jeji suke wasa.21. Tana kwanciya a ƙarƙashin inuwar itacen lotus ta ɓuya cikin kyauro da fadama.22. Inuwa ta rufe ta da ƙaddaji, itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.23. Sa’ad da kogi ya cika yana hauka, ba tă damu ba; ba abin da zai same ta ko da a gaban bakinta Urdun yake wucewa.24. Ko akwai wanda zai iya kama ta ba ta kallo, ko kuma a kama ta da tarko a huda hancinta?Zabura 101:1-41. Zan rera wa ƙauna da adalcinka; gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo.2. Zan yi hankali ga yin rayuwa marar zargi, yaushe za ka zo gare ni? Zan bi da sha’anin gidana da zuciya marar abin zargi3. Ba zan kafa a gaban idanuna 1 wani abu marar kyau ba. Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci; ba za su manne mini ba.4. Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni; ba abin da zai haɗa ni da mugunta.Karin Magana 23:29-3029. Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki? Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu?30. Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi, waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi.1 Korintiyawa 6:1-201. In wani a cikinku yana da damuwa da wani, don me zai kai ƙara a gaban marasa bi, maimakon yă kai ƙara a gaban tsarkaka?2. Ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a ba? In kuwa za ku yi wa duniya shari’a, ai, kun isa ku yi shari’a a kan ƙananan damuwoyi ke nan.3. Ba ku san cewa za mu yi wa mala’iku shari’a ba? Balle al’amuran da suka shafi duniyan nan!4. Saboda haka, in kuna da damuwa game da irin waɗannan al’amura, sai ku naɗa alƙalai ko cikin waɗanda ba kome ba ne a ikkilisiya!5. Na faɗi haka ne don ku ji kunya. Ashe, ba za a iya samun wani a cikinku mai hikima wanda zai iya sasanta tsakanin masu bi ba?6. Me zai sa ɗan’uwa yă kai ƙarar ɗan’uwa, a gaban marasa bi?7. Ƙarar junanku ma da kuke yi, ai, kāsawa ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura ko an zambace ku?8. Amma ga shi ku da kanku kuna cuta, kuna kuma zamba, har ma ga ’yan’uwanku ne kuke yi wannan.9. Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu,10. ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah.11. Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.12. “Ina da dama in yi kome,” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ina da dama in yi kome” sai dai ba abin da zai mallake ni.13. “An yi abinci domin ciki ne, ciki kuma domin abinci.” Amma Allah zai hallaka su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki.14. Ta wurin ikonsa, Allah ya tashe Ubangiji daga matattu, haka zai tashe mu mu ma.15. Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Kiristi ne kansa? Zai kyautu in ɗauki gaɓoɓin Kiristi in haɗa da jikin karuwa? Sam!16. Ba ku san cewa shi wanda ya haɗa jikinsa da karuwa sun zama ɗaya a cikin jiki ke nan ba? Gama an ce, “Biyun za su zama jiki ɗaya.”17. Wanda kuwa ya haɗa jikinsa da Ubangiji ya zama ɗaya da shi ke nan a ruhu.18. Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne.19. Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne;20. saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.