Baibul a cikin shekara guda Agusta 25Ayuba 41:1-341. “Ko za ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kamar kifi ko kuma ka daure harshenta da igiya?2. Za ka iya sa igiya a cikin hancinta ko kuma ka huda muƙamuƙanta da ƙugiya?3. Za tă ci gaba da roƙonka ka yi mata jinƙai? Ko za tă yi maka magana a hankali?4. Za tă yi yarjejjeniya da kai don ka ɗauke ta tă zama baiwa gare ka dukan kwanakin ranta?5. Za ka yi wasa da ita kamar yadda za ka yi da tsuntsu? Ko za ka daure ta da tsirkiya domin bayinka mata?6. ’Yan kasuwa za su saye ta ko za su raba ta a tsakaninsu?7. Ko za ka iya huda fatarta da kibiya ka kuma huda kansa da māsu?8. In ka ɗora hannunka sau ɗaya a kanta za ka tuna da yaƙin da ba za ka sāke yi ba!9. Duk ƙoƙarin kama ta banza ne; ganin ta kawai abin tsoro ne.10. Ba wanda ya isa yă tsokane ta. Wane ne kuma ya isa yă yi tsayayya da ni?11. Wane ne yake bi na bashi da dole in biya? Duk abin da yake ƙarƙashin sama nawa ne.12. “Ba zan daina magana game da gaɓoɓinta ba ƙarfinta da kuma kyan kamanninta ba.13. Wa zai iya tuɓe mata mayafinta? Wa zai iya shiga tsakanin ɓawonta.14. Wa zai iya buɗe ƙofofin bakinta? Haƙoranta ma abin tsoro ne?15. An rufe bayanta da jerin garkuwoyi aka manne su sosai.16. Suna kurkusa da juna yadda da ƙyar iska take iya wucewa tsakani.17. An haɗa su da juna sun mannu da juna kuma ba za a iya raba su ba.18. Numfashinta yana fitar da wuta; idanunta kamar hasken zuwan safe.19. Wuta tana fitowa daga bakinta; tartsatsin wuta suna fitowa,20. Hayaƙi yana fitowa daga hancinta kamar daga tukunya mai tafasa a kan wutar itace.21. Numfashinta yana sa garwashi yă kama wuta, harshen wuta yana fita daga bakinta.22. Akwai ƙarfi a cikin wuyanta; razana tana wucewa a gabanta.23. Namanta yana da kauri a manne da juna; naman yana da tauri ba ya matsawa.24. Ƙirjinta yana da ƙarfi kamar dutse, da ƙarfi kamar dutsen niƙa.25. Sa’ad da ta tashi, manya suna tsorata; suna ja da baya.26. Takobi ba ta iya yankanta, kibiya ko māshi ba sa iya huda ta.27. Ƙarfe kamar kara ne a wurinta tagulla kuma kamar ruɓaɓɓen katako ne a wurinta.28. Māsu ba su sa ta tă gudu; jifar majajjawa kamar na ciyawa ne gare ta.29. Kulki a gare ta kamar ciyawa ne, tana dariyar wucewar māshi.30. Cikinta yana rufe a ɓawo masu ƙarfi, tana kabtar ƙasa in tana tafiya.31. Tana sa zurfin kogi yă tafasa kamar tukunya, ta kuma sa teku yă zama kamar tukunyar man shafawa.32. A bayanta ya bar haske kamar zurfin ruwan da yana kumfa.33. Ba wani abu kamar ta a duniya, halitta marar tsoro.34. Tana rena duk masu girman kai. Ita take mulki kan duk masu girman kai.”Ayuba 42:1-171. Sa’an nan Ayuba ya amsa wa Ubangiji,2. “Na san cewa za ka iya yin dukan abubuwa; ba wanda zai iya ɓata shirinka.3. Ka yi tambaya, ‘Wane ne wannan da ya ƙi karɓar shawarata shi marar ilimi?’ Ba shakka na yi magana game da abubuwan da ban gane ba, abubuwan ban al’ajabi da sun fi ƙarfin ganewata.4. “Ka ce, ‘Saurara yanzu, zan kuma yi magana zan tambaye ka, kuma za ka amsa mini.’5. Kunnuwana sun ji game da kai amma yanzu na gan ka.6. Saboda haka na rena kaina na kuma tuba cikin ƙura da toka.”7. Bayan Ubangiji ya gaya wa Ayuba waɗannan abubuwa, ya ce wa Elifaz mutumin Teman, “Ina fushi da kai da abokanka guda biyu domin ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.8. Saboda haka yanzu sai ku ɗauki bijimai guda bakwai, da raguna bakwai, ku je wurin bawana Ayuba ku miƙa hadaya ta ƙonawa domin kanku. Bawana Ayuba zai yi muku addu’a zan kuwa karɓi addu’arsa in bi da ku nisa da wawancinku. Ba ku faɗi abin da yake daidai game da ni ba yadda bawana Ayuba ya yi ba.”9. Saboda haka Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa da Zofar mutumin Na’ama, suka yi abin da Ubangiji ya gaya masu; Ubangiji kuma ya karɓi addu’ar Ayuba.10. Bayan Ayuba ya yi wa abokansa addu’a, Ubangiji ya sa shi ya sāke zama mai arziki ya ninka abin da yake da shi a dā sau biyu.11. Dukan ’yan’uwansa maza da mata da duk waɗanda suka san shi a dā suka zo suka ci abinci tare da shi a cikin gidansa. Suka ta’azantar da shi suka ƙarfafa shi game da duk wahalar da Ubangiji ya auka masa, kowannensu kuma ya ba shi azurfa da zobe na zinariya.12. Ubangiji ya albarkaci ƙarshen Ayuba fiye da farkonsa. Yana da tumaki guda dubu goma sha huɗu, raƙuma guda dubu shida; shanun noma guda dubu da jakuna guda dubu.13. Ya kuma haifi ’ya’ya maza bakwai, mata uku.14. ’Yar farko ya kira ta Yemima, ta biyun Keziya ta ukun Keren-Haffuk.15. Duk a cikin ƙasar ba a samu kyawawan mata kamar ’ya’yan Ayuba ba, kuma babansu ya ba su gādo tare ta ’yan’uwansu maza.16. Bayan wannan Ayuba ya rayu shekara ɗari da arba’in; ya ga ’ya’yansa da ’ya’yansu har tsara ta huɗu.17. Sa’an nan Ayuba ya rasu da kyakkyawan tsufa.Zabura 101:5-85. Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye shi za a kashe; duk mai renin wayo da mai girman kai, ba zan jure masa ba.6. Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar, don su zauna tare da ni; tafiyarsa ba ta da zargi zai yi mini hidima.7. Babu mai ruɗun da zai zauna a gidana; babu mai ƙaryan da zai tsaya a gabana.8. Kowace safiya zan rufe bakunan dukan mugaye a ƙasar; zan yanke kowane mai aikata mugunta daga birnin Ubangiji.Karin Magana 23:31-3531. Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!32. A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa.33. Idanunka za su riƙa gane-gane, zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa.34. Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna, kwance a sama itacen jirgin ruwa.35. Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba! Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa! Yaushe zan farka don in ƙara shan wani?”1 Korintiyawa 7:1-191. To, game da zancen da kuka rubuto. Yana da kyau mutum yă zauna ba aure.2. Amma da yake fasikanci ya yi yawa, ya kamata kowane mutum yă kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta.3. Ya kamata miji yă cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta.4. Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma.5. Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yă jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku.6. Wannan fa shawara ce nake ba ku, ba umarni ba.7. Da ma a ce dukan maza kamar ni suke mana. Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa; wani yana da wannan baiwa, wani kuwa wancan.8. To, ga marasa aure da gwauraye kuwa ina cewa yana da kyau su zauna haka ba aure, yadda nake.9. Sai dai in ba za su iya ƙame kansu ba, to, su yi aure, don yă fi kyau a yi aure, da sha’awa ta sha kan mutum.10. Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa kada mace ta rabu da mijinta.11. In kuwa ta rabu da shi, sai ta kasance ba aure, ko kuma ta sāke shiryawa da mijinta. Kada miji kuma yă saki matarsa.12. Ga sauran kuwa (ni ne fa na ce ba Ubangiji ba), in wani ɗan’uwa yana da mata wadda ba mai bi ba ce, kuma tana so ta zauna tare da shi, kada yă sake ta.13. In kuma mace tana da miji wanda ba mai bi ba ne, kuma yana so yă zauna tare da ita, kada tă kashe auren.14. Don miji marar ba da gaskiya an tsarkake shi ta wurin matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma an tsarkake ta ta wurin mijinta. In ba haka ba ’ya’yanku ba za su zama da tsarki ba, amma kamar yadda yake, su masu tsarki ne.15. Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne.16. Ke mace, kin sani ne, ko ke ce za ki ceci mijinki? Kai miji, ka sani ne, ko kai ne za ka ceci matarka?17. Duk da haka, sai kowa yă kasance a rayuwar da Ubangiji ya sa shi da kuma wanda Allah ya kira shi. Umarnin da na kafa a dukan ikkilisiyoyi ke nan.18. In an riga an yi wa mutum kaciya sa’ad da aka kira shi, to, kada yă zama marar kaciya. In an kira mutum sa’ad da yake marar kaciya, to, kada a yi masa kaciya.19. Kaciya ba wani abu ba ne, rashin kaciya kuma ba wani abu ba ne. Kiyaye umarnin Allah shi ne muhimmin abu. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.