Baibul a cikin shekara guda Agusta 27Mai Hadishi 3:1-221. Akwai lokaci domin kowane abu, da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.2. Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa, lokacin shuki da lokacin tumɓukewa.3. Lokacin kisa da lokacin warkarwa, lokacin rushewa da lokacin ginawa.4. Lokacin kuka da lokacin dariya, lokacin makoki da lokacin rawa.5. Lokacin warwatsa duwatsu da lokacin tara su, lokacin runguma da lokacin dainawa.6. Lokacin nema, da lokacin fid da zuciya, lokacin ajiyewa da lokacin zubarwa.7. Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa, lokacin yin shiru da lokacin magana.8. Lokacin ƙauna da lokacin ƙiyayya, lokacin yaƙi da lokacin salama.9. Wace riba ce ma’aikaci yake da ita saboda wahalarsa?10. Na ga nawayar da Allah ya ɗora a kan mutane.11. Ya yi kowane abu da kyau a lokacinsa. Ya kuma sa matuƙa a zukatan mutane, duk da haka sun kāsa gane abin da Allah ya yi daga farko zuwa ƙarshe.12. Na san ba abin da ya fi wa mutane kyau fiye da su ji daɗi su kuma yi alheri yayinda suke da rai.13. Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce.14. Na san cewa duk abin da Allah ya yi zai dawwama har abada; ba abin da za a ƙara ko a rage. Allah ya yi haka domin mutane su girmama shi.15. Duk abin da yana nan ya taɓa kasancewa, kuma abin da zai kasance, ya taɓa kasancewa; Allah kuma zai nemi bayanin abubuwan da suka wuce.16. Sai na ga wani abu kuma a duniya, a wurin shari’a, akwai mugunta a can, a wurin adalci, akwai mugunta a can.17. Sai na yi tunani a zuciyata, “Allah zai shari’anta masu adalci da masu mugunta, gama za a kasance da lokaci domin kowane aiki, lokaci domin kowane abu.”18. Na sāke yin tunani, “Game da mutane kam, Allah kan gwada su don su san cewa ba su fi dabba ba.19. Ƙaddarar mutum ɗaya take da ta dabba; ƙaddara ɗaya ce take jiransu biyu. Yadda ɗayan yake mutuwa, haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne; mutum bai fi dabba ba. Kowane abu ba shi da amfani.20. Duka wuri ɗaya za su tafi; gama duka daga turɓaya suka fito, kuma ga turɓaya duka za su koma.21. Wa ya tabbatar cewa ruhun mutum yakan tashi sama sa’an nan na dabba yă sauka ƙasa?”22. Saboda haka na ga babu abin da ya fi kyau wa mutum fiye da yă more wahalar aikinsa, domin wannan ne rabonsa. Gama wa zai kawo shi yă ga abin da zai faru a bayansa?Zabura 102:12-1712. Amma kai, ya Ubangiji, kana zaune a kursiyinka har abada; sunan da ka yi zai dawwama a dukan zamanai.13. Za ka tashi ka kuma ji tausayin Sihiyona, gama lokaci ne na nuna alheri gare ta; ƙayyadadden lokacin ya zo.14. Gama duwatsunta suna da daraja ga bayinka; ƙurarta kawai kan sa su ji tausayi.15. Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji, dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka.16. Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyona ya kuma bayyana a ɗaukakarsa.17. Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi; ba zai ƙyale roƙonsu ba.Karin Magana 24:3-43. Ta wurin hikima ce ake gina gida, kuma ta wurin fahimi ake kafa ta;4. ta wurin sani ɗakunanta sukan cika da kyawawan kayayyaki masu daraja.1 Korintiyawa 8:1-131. To, game da abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa. Mun san cewa dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kawo girman kai, amma ƙauna takan gina.2. Mutumin da yake tsammani ya san abu, sanin da yake da shi bai isa ba.3. Amma mutumin da yake ƙaunar Allah, Allah yana sane da shi.4. To, game da cin abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa, mun san cewa “Gunki ba kome ba ne a duniya”, kuma “Babu wani Allah sai dai ɗaya.”5. Gama ko da akwai abubuwan da ake ce da su alloli, a sama ko a ƙasa (don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa),6. duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.7. Amma ba kowa ne ya san wannan ba. Har yanzu, waɗansu mutane sun saba da tunani cewa gumaka ainihi ne, saboda haka sa’ad da suka ci irin abincin nan, sukan ɗauka cewa kamar an miƙa wa ga gunki ne, kuma da yake lamirinsu ba ƙarfi, yakan ƙazantu.8. Gaskiya ne cewa ba ma samun yardar Allah ta wurin abin da muke ci. Ba ma rasa wani abu idan ba mu ci ba, kuma ba ma ƙaru da wani abu in muka ci.9. Sai dai ku yi hankali, kada yin amfani da ’yancinku yă zama abin sa tuntuɓe ga marasa ƙarfi.10. Gama in wani wanda lamirinsa ba shi da ƙarfi ya gan ka, kai da kake da wannan sani, kana ci a haikalin gumaka, ashe, ba zai sami ƙarfin halin cin abin da aka miƙa wa gumaka ba?11. Saboda haka ta wurin sanin nan naka sai ka sa wannan ɗan’uwa marar ƙarfi wanda Kiristi ya mutu dominsa yă hallaka.12. Sa’ad da ka rushe lamiri mai bi marar ƙarfi, ka yi wa Kiristi zunubi ke nan.13. Saboda haka, in abin da nake ci zai sa ɗan’uwana yă yi zunubi, ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa shi yă yi tuntuɓe. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.