Baibul a cikin shekara guda Agusta 29Mai Hadishi 7:1-291. Suna mai kyau ya fi turare mai ƙanshi, kuma ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa.2. Gara a tafi gidan makoki da a je gidan biki, gama mutuwa ce ƙaddarar kowane mutum; ya kamata masu rai su lura da haka.3. Baƙin ciki ya fi dariya, gama baƙin ciki yakan kawo gyara.4. Zuciyar masu hikima tana a gidan makoki, amma zuciya wawaye tana a gidan shagali.5. Gara ka saurari tsawatawar mai hikima da ka saurari waƙar wawaye.6. Kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya, haka dariyar wawaye take. Wannan ma ba shi da amfani.7. Zalunci yakan mai da mutum mai hikima wawa, cin hanci kuma yakan lalace hali.8. Ƙarshen abu ya fi farkonsa, haƙuri kuma ya fi girman kai.9. Kada ranka yă yi saurin tashi, gama fushi yana zama a cinyar wawaye.10. Kada ka ce, “Me ya sa kwanakin dā sun fi waɗannan?” Gama ba daidai ba ne a yi irin waɗannan tambayoyi.11. Hikima, kamar gādo, abu mai kyau ne tana kuma da amfani ga waɗanda suka ga rana.12. Hikima mafaka ce takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi. Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita ita ce amfanin ilimi.13. Ku lura da abin da Allah ya yi. Wa zai iya miƙe abin da ya tanƙware?14. Sa’ad da al’amura suke tafiya daidai, ka yi farin ciki, amma sa’ad da suka lalace, ka tuna, Allah ne ya yi wancan shi ne kuma ya yi wannan. Saboda haka, mutum ba zai san wani abu game da nan gabansa ba.15. A cikin rayuwan nan ta rashin amfani nawa, na lura da waɗannan abubuwa biyu, mai adalci yana hallakawa cikin adalcinsa, mai mugunta kuma yana tsawon rai cikin muguntarsa.16. Kada ka cika yin adalci, fiye da kima, kada kuma ka cika yin hikima, don me za ka hallaka kanka!17. Kada ka cika yin mugunta, kada kuma ka cika yin wauta, don me za ka mutu kafin lokacinka?18. Yana da kyau ka kama ɗaya ba tare da ka saki wancan ba. Mai tsoron Allah zai guji wuce gona da iri.19. Hikima takan sa mutum guda mai hikima yă yi ƙarfi fiye da masu mulki goma a cikin birni.20. Babu mai adalci a duniya wanda yake yin abin da yake daidai da bai taɓa yin zunubi ba.21. Kada ka mai da hankali ga dukan abin da mutane suke faɗi, in ba haka ba wata rana za ka ji bayinka suna zaginka.22. Gama kai kanka ka sani cewa sau da yawa ka zagi waɗansu.23. Dukan waɗannan na gwada su ta wurin hikima na kuma ce, “Na ƙudurta in zama mai hikima,” amma abin ya fi ƙarfina.24. Ko da me hikima take, Abin ya yi mana zurfi ƙwarai, yana da wuyar ganewa, wa zai iya gane shi?25. Saboda haka na mai da hankalina ga fahimi, don in bincika in nemi hikima da yadda aka tsara abubuwa, in kuma fahimci wawancin mugunta da haukar wauta.26. Sai na iske wani abin da ya fi mutuwa ɗaci mace wadda take tarko ne, wadda zuciyarta tarko ne wadda kuma hannuwanta sarƙa ne. Mutumin da ya gamshi Allah zai tsere mata, amma za tă kama mai zunubi.27. Malami ya ce, “Duba, abin da na gane ke nan. “Na tara abu guda da wani, don in gane tsarin abubuwa,28. yayinda nake cikin nema amma ban samu ba, sai na sami adali guda cikin dubu, amma ba mace mai adalci guda a cikinsu duka.29. Wannan ne kaɗai abin da na gane. Allah ya yi mutum tsab amma sai muka rikitar da kanmu.”Zabura 102:1-51. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; bari kukata ta neman taimako ta zo gare ka.2. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni sa’ad da nake cikin damuwa. Ka juye kunnenka gare ni; sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri.3. Gama kwanakina sun ɓace kamar hayaƙi; ƙasusuwana suna ƙuna kamar jan wuta.4. Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa; na manta in ci abinci.5. Saboda nishina mai ƙarfi na rame na bar ƙasusuwa kawai.Karin Magana 24:7-97. Hikima ta yi wa wawa nisa ƙwarai a cikin taro a ƙofar gari ba shi da ta cewa.8. Duk mai ƙulla mugunta za a ɗauka shi mai kuta hargitsi ne.9. Makircin wawa zunubi ne, mutane kuma sukan yi ƙyamar mai ba’a.1 Korintiyawa 10:1-181. Ba na so ku kasance da rashin sani, ’yan’uwa, cewa dukan kakannin-kakanninmu sun yi tafiya a ƙarƙashin girgije, dukansu kuma suka bi ta tsakiyar teku.2. An yi wa dukansu baftisma ga bin Musa a cikin girgije da kuma cikin teku.3. Dukansu sun ci abincin ruhaniya guda4. suka kuma sha ruwan ruhaniyan nan guda; gama sun sha daga dutsen ruhaniya nan, wanda ya yi tafiya tare da su, wannan dutsen kuwa Kiristi ne.5. Duk da haka, Allah bai ji daɗin yawancinsu ba; gawawwakinsu kuwa suka bazu ko’ina a cikin hamada.6. To, waɗannan abubuwa misalai ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi.7. Kada ku zama masu bautar gumaka, yadda waɗansunsu suka zama; kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mutanen suka zauna don su ci su kuma sha, suka kuma tashi suka shiga rawa ta rashin kunya.”8. Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har a rana guda mutane dubu ashirin da uku a cikinsu suka mutu.9. Kada mu gwada Kiristi yadda waɗansunsu suka yi, har macizai suka kakkashe su.10. Kada kuma ku yi gunaguni yadda waɗansunsu suka yi, har mala’ika mai hallakarwa ya hallaka su.11. Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana.12. Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi!13. Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.14. Saboda haka abokaina ƙaunatattu, ku guje wa bautar gumaka.15. Ina magana da ku a kan ku mutane ne fa masu azanci; ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa.16. Kwaf nan na godiya da muke yin godiya da shi, ashe ba tarayya ce a cikin jinin Kiristi ba? Wannan burodi kuma da muke karya mu ci, ashe, ba tarayya ne a cikin jikin Kiristi ba?17. Da yake burodin nan ɗaya ne, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama dukanmu muna ci daga burodi nan guda.18. Ku dubi mutanen Isra’ila mana. Ashe, waɗanda suke cin hadayu, ba ɗaya suke da juna cikin cin hadayun da aka miƙa a bagade ba? Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.