Baibul a cikin shekara guda Agusta 31Mai Hadishi 11:1-101. Ka jefa burodinka a bisa ruwaye, gama bayan kwanaki masu yawa, za ka sāke samunsa.2. Ka raba abin hannunka ga mutum bakwai, I, har ma takwas, gama ba ka san bala’in da zai auko wa ƙasar ba.3. In gizagizai sun cika da ruwa, sukan zub da ruwan sama bisa duniya. Itace ya fāɗi, ko wajen kudu ne, ko wajen arewa, inda ya fāɗi a nan zai kwanta.4. Duk mai la’akari da iska, ba zai yi shuka ba, mai la’akari da gizagizai kuma, ba zai yi girbi ba.5. Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba, ko yadda aka siffanta jiki a cikin mahaifiya, haka ba za ka fahimci aikin Allah Mahaliccin dukan abubuwa ba.6. Ka shuka irinka da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka.7. Haske da yana da kyau, abu mai kyau ne kuma idanu su dubi rana.8. Kome tsawon rayuwar mutum, bari yă more su duka. Amma bari kuma yă tuna da kwanakin duhu, gama su ma za su yi yawa. Duk abin da zai faru ba shi da amfani.9. Ka yi murna, kai matashi, a ƙuruciyarka, bari zuciyarka kuma tă yi farin ciki a kwanakin ƙuruciyarka. Ka bi shawarar zuciyarka da kuma duk abin da idanunka suka gani, amma ka sani fa, cikin dukan al’amuran nan Allah zai shari’anta ka.10. Saboda haka, ka fid da tsoro daga zuciyarka ka kakkaɓe duk wani abin da ya dami rayuwarka, gama ƙuruciya da ƙarfi ba su da amfani.Mai Hadishi 12:1-141. Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin ƙuruciyarka, kafin lokacin wahala ta zo shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce, “Ba na jin daɗinsu,”2. kafin rana da haske wata da taurari su daina haske, gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙa ruwa;3. sa’ad da masu tsaron gida suke rawar jiki, majiya ƙarfi kuma suka rasa ƙarfi, sa’ad da masu niƙa suka daina don ba su da yawa, idanun da suke duba ta taga suka duhunta;4. sa’ad da aka rufe ƙofofin shiga tituna ƙarar niƙa kuma ya tsagaita; sa’ad da kukan tsuntsaye ta farkar da mutane, ba a kuwa jin waƙoƙinsu,5. sa’ad da mutane suke jin tsoron tudu da kuma hatsarori a tituna; sa’ad da itacen almon ya toho, fāra kuma ya yi ta jan jikinsa da ƙyar, sha’awace-sha’awace sun kafe. Daga nan mutum ya tafi madawwamiyar gidansa ya bar masu makoki suna ta yi.6. Ka tuna da shi, kafin igiyar azurfa ta katse, ko tasar zinariya ta fashe; kafin tulu yă ragargaje a maɓulɓula, ko guga ta tsinke a rijiya,7. turɓaya ta koma ƙasar da ta fito, rai kuma yă koma ga Allah wanda ya ba da shi.8. “Ba amfani! Ba amfani!” In ji Malami, “Gaba ɗaya ba amfani!”9. Ba kawai Malami ya kasance mai hikima ba, amma kuma ya koyar da mutane. Ya yi tunani ya kuma yi binciken da ya tsara karin magana masu yawa.10. Malami ya yi bincike don yă sami kalmomin da suka dace, kuma abin da ya rubuta daidai ne da kuma gaskiya.11. Kalmomin masu hikima kamar tsinken tsokanar dabba ne, tarin maganganunsu kuma kamar ƙusoshi ne da aka kafa daram, da aka ba wa Makiyayi guda.12. Ka yi hankali ɗana, game da duk wani ƙari a kan waɗannan. Wallafa littattafai ba shi da iyaka, kuma yawan karatu yakan gajiyar da jiki.13. Yanzu an ji kome; ga ƙarshen magana. Ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye umarnansa, gama wannan shi ne dukan hakkin mutum.14. Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki, har da waɗanda aka yi a ɓoye, ko nagari ne, ko mugu.Zabura 103:15-2215. Game da mutum dai, kwanakinsa suna kamar ciyawa da suke haɓaka kamar fure a gona;16. iska kan hura a kansa sai ya ɓace ba a kuwa sāke tuna da inda dā yake.17. Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,18. tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.19. Ubangiji ya kafa kursiyinsa a sama, masarautarsa kuwa na mulki a bisa duka.20. Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa, ku jarumawa masu yi masa aiki, waɗanda suke yin biyayya da maganarsa.21. Yabi Ubangiji, dukanku rundunarsa ta sama, ku bayinsa waɗanda kuke aikata nufinsa.22. Yabi Ubangiji, dukanku ayyukansa ko’ina a mulkinsa. Yabi Ubangiji, ya raina.Karin Magana 24:13-1413. Ka sha zuma, ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau; zuma daga kaki yana da zaƙi a harshenka.14. Ka kuma san cewa hikima tana da zaƙi ga rai; in ka same ta, akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.1 Korintiyawa 11:1-161. Ku bi gurbina, kamar yadda ni nake bin gurbin Kiristi.2. Ina yabonku saboda kuna tunawa da ni a cikin kowane abu, kuna kuma riƙe da koyarwar, yadda na ba ku.3. To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne.4. Kowane namijin da ya yi addu’a ko annabci da kansa a rufe ya jawo kunya wa kansa.5. Duk macen da ta yi addu’a ko annabci da kanta a buɗe kuwa ta rena kanta, ya zama kamar an aske kanta ke nan.6. In mace ba ta so tă rufe kanta, to, sai tă aske gashinta; in kuwa abin kunya ne mace tă yanke ko tă aske gashinta, to, sai tă rufe kanta.7. Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba, da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne.8. Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji.9. Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.10. Don haka, saboda wannan, da kuma saboda mala’iku, dole mace ta ɗaura wani abu a kanta.11. Duk da haka a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, namiji kuma ba a rabe yake da mace ba.12. Kamar yadda mace ta fito daga namiji, haka kuma aka haifi namiji ta wurin mace. Sai dai kowane abu daga Allah yake.13. Ku kanku duba mana. Ya yi kyau mace tă yi addu’a ga Allah da kanta a buɗe?14. Kai, yadda halitta take ma, ai, ta koya muku cewa in namiji yana da dogon gashi, abin kunya ne a gare shi,15. amma in mace tana da dogon gashi, ai, daraja ce a gare ta. Gama an ba ta dogon gashi saboda rufe kanta ne.16. In akwai mai gardama da wannan, to, mu dai ba mu da wata al’ada, haka ma ikkilisiyoyin Allah. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.