Baibul a cikin shekara guda Agusta 9Ayuba 9:1-351. Sai Ayuba ya amsa,2. “Lalle, na san wannan gaskiya ne. Amma ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?3. Ko da mutum yana so yă yi gardama da shi, ba zai taɓa amsa masa ba ko da sau ɗaya cikin dubu.4. Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa. Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara?5. Yana matsar da manyan duwatsu kafin su sani kuma yana juya su cikin fushinsa.6. Yana girgiza ƙasa, yana girgiza harsashenta.7. Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske; yana hana taurari yin haske.8. Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai ya kuma yi tafiya a kan raƙuman ruwan teku.9. Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza, da ’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu.10. Yana yin abubuwan banmamaki waɗanda ba a iya ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a iya ƙirgawa.11. Ba na iya ganinsa lokacin da ya wuce ni; ba na sani ya wuce lokacin da ya wuce.12. Wane ne ya isa yă hana shi in ya ƙwace abu? Wa zai ce masa, ‘Me kake yi?’13. Allah ba ya danne fushinsa; ko dodannin ruwan da ake kira ayarin Rahab ya tattake su.14. “Ta yaya zan iya yin faɗa da shi? Ina zan iya samun kalmomin da zan yi gardama da shi?15. Ko da yake ba ni da laifi, ba zan iya amsa masa ba; sai dai roƙon jinƙai zan iya yi ga mahukuncina.16. Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini, ban yarda cewa zai saurare ni ba.17. Zai sa hadari yă danne ni yă ƙara mini ciwona ba dalili.18. Ba zai bari in yi numfashi ba, sai dai yă ƙara mini azaba.19. In maganar ƙarfi ne, shi babban mai ƙarfi ne! In kuma maganar shari’a ne, wa zai kai kararsa?20. Ko da ni marar ƙarfi ne, bakina ya isa yă sa in zama mai laifi; in ba ni da laifi, zai sa in yi laifi.21. “Ko da yake ba ni da laifi, ban damu da kaina ba; na rena raina.22. Ba bambanci; shi ya sa na ce, ‘Yana hallaka marasa laifi da kuma mugaye.’23. Lokacin da bala’i ya kawo ga mutuwa, yakan yi dariyar baƙin cikin marasa laifi.24. Lokacin da ƙasa ta faɗa a hannun mugaye, yakan rufe idanun masu shari’a. In ba shi ba wa zai yi wannan?25. “Kwanakina sun fi mai gudu wucewa da sauri; suna firiya babu wani abin jin daɗi a cikinsu.26. Suna wucewa kamar jirgin ruwan da aka yi da kyauro, kamar jahurma da ta kai wa namanta cafka.27. ‘In na ce zan manta da abin da yake damu na, zan yi murmushi in daina nuna ɓacin rai,’28. duk da haka ina tsoron duk wahalata, domin na san ba za ka ɗauke ni marar laifi ba.29. Tun da an riga an ɗauke ni mai laifi, duk ƙoƙarina a banza yake.30. Ko da na wanke jikina duka da sabulu, na wanke hannuwana kuma da soda,31. duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri, yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni.32. “Shi ba mutum ba ne kamar ni wanda zan iya amsa masa, har da za mu yi faɗa da juna a wurin shari’a.33. In da akwai wanda zai iya shiga tsakaninmu, ya ɗora hannunsa a kanmu tare,34. wani wanda zai sa Allah yă daina duka na, don yă daina ba ni tsoro.35. Sa’an nan ne zan iya yin magana ba tare da jin tsoronsa ba, amma a yadda nake a yanzu ba zan iya ba.Ayuba 10:1-221. “Na gaji da rayuwa; saboda haka bari in faɗi zuciyata gabagadi yadda raina yake jin ba daɗi.2. Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni, amma ka gaya mini laifin da na yi maka.3. Kana jin daɗin ba ni wahala, don me ka yashe ni, abin da ka halitta da hannunka, yayinda kake murmushi game da shirye-shiryen mugaye?4. Idanunka irin na mutum ne? Kana gani yadda mutum yake gani ne?5. Kwanakinka kamar na mutane ne, ko shekarunka kamar na mutane ne6. da za ka neme ni da laifi ka hukunta ni?7. Ko da yake ka san ba ni da laifi, kuma ba wanda zai iya cetona daga hannunka.8. “Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni. Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni?9. Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu. Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma?10. Ba kai ka zuba ni kamar madara ba, na daskare kamar cuku.11. Ka rufe ni da tsoka da fata, ka harhaɗa ni da ƙasusuwa da jijiyoyi?12. Ka ba ni rai ka kuma yi mini alheri, kuma cikin tanadinka ka kula da ruhuna.13. “Amma wannan shi ne abin da ka ɓoye a zuciyarka, na kuma san abin da yake cikin zuciyarka ke nan.14. In na yi zunubi kana kallo na kuma ba za ka fasa ba ni horo ba don laifin da na yi.15. Idan ina da laifi, kaitona! Ko da ba ni da laifi, ba zan iya ɗaga fuskata ba, gama kunya ta ishe ni duk ɓacin rai ya ishe ni.16. In na ɗaga kaina, za ka neme ni kamar zaki ka sāke nuna al’ajabin ikonka a kaina.17. Kana sāke kawo sababbin waɗanda za su ba da shaida a kaina kana ƙara haushinka a kaina; kana ƙara kawo mini hari.18. “Me ya sa ka fito da ni daga cikin uwata? Da ma na mutu kafin a haife ni.19. Da ma ba a halicce ni ba, da na mutu tun daga cikin cikin uwata na wuce zuwa kabari!20. ’Yan kwanakina ba su kusa ƙarewa ba ne? Ka rabu da ni don in ɗan samu sukuni na ɗan lokaci21. kafin in koma inda na fito, ƙasa mai duhu da inuwa sosai,22. zuwa ƙasa mai duhun gaske, da inuwa da hargitsi, inda haske yake kamar duhu.”Zabura 93:1-51. Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka; Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi. An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba.2. An kafa kursiyin tun da daɗewa; kana nan tun fil azal.3. Tekuna sun taso, ya Ubangiji, tekuna sun ta da muryarsu; tekuna sun tā da ta raƙumansu masu tumbatsa.4. Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye, mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku, Ubangiji mai zama a bisa mai girma ne.5. Ƙa’idodinka suna nan daram; tsarki ya yi wa gidanka ado har kwanaki marar ƙarewa, ya Ubangiji.Karin Magana 22:22-2322. Kada ka zalunci matalauta a kan suna matalauta kada kuma ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari’a,23. gama Ubangiji zai yi magana dominsu zai kuwa washe waɗanda suka washe su.Romawa 9:16-3316. Saboda haka, bai danganta ga sha’awar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah.17. Gama Nassi ya ce wa Fir’auna, “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.”18. Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so.19. Waninku zai iya ce mini, “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?”20. Amma wane ne kai, ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’ ”21. Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yă gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja?22. Haka ma aikin Allah yake. Ya so yă nuna fushinsa yă kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa, waɗanda aka shirya domin hallaka?23. Haka kuma ya so yă sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka24. har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Al’ummai?25. Kamar yadda ya faɗa a Hosiya. “Zan kira su ‘mutanena,’ su da ba mutanena ba; zan kuma kira ta ‘ƙaunatacciyata,’ ita da ba ƙaunatacciyata ba,”26. kuma, “Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba,’ za a ce da su, ‘’ya’yan Allah mai rai.’ ”27. Ishaya ya ɗaga murya game da Isra’ila ya ce, “Ko da yake yawan Isra’ilawa yana kama da yashi a bakin teku, ragowa ce kaɗai za su sami ceto.28. Gama Ubangiji zai zartar da hukuncinsa a bisan duniya da sauri kuma ba da ɓata lokaci ba.”29. Yana nan kamar yadda Ishaya ya riga ya faɗa. “Da ba don Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana zuriya ba, da mun zama kamar Sodom, da mun kuma zama kamar Gomorra.”30. Me za mu ce ke nan? Ai, Al’ummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya;31. amma Isra’ila da suka yi ƙwazo wajen bin Dokar adalci, ba su same shi ba.32. Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen binta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.”33. Kamar yadda yake a rubuce, “Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓe da kuma dutsen da yake sa su fāɗi wanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.