Baibul a cikin shekara guda Satumba 1Waƙar Waƙoƙi 1:1-171. Waƙar Waƙoƙin Solomon.2. Bari yă sumbace ni da sumbar bakinsa, gama ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi.3. Ƙanshin turarenka mai daɗi ne; sunanka kuwa kamar turaren da aka tsiyaye ne. Shi ya sa mata suke ƙaunarka!4. Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri! Bari sarki yă kai ni gidansa. Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai, za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi. Daidai ne su girmama ka!5. Ni baƙa ce, duk da haka kyakkyawa. Ya ku ’yan matan Urushalima, ni baƙa ce kamar tentunan Kedar, kamar labulen tentin Solomon.6. Kada ku harare ni domin ni baƙa ce, gama rana ta dafa ni na yi baƙa. ’Ya’yan mahaifiyata maza sun yi fushi da ni suka sa ni aiki a gonakin inabi; na ƙyale gonar inabi na kaina.7. Faɗa mini, kai da nake ƙauna, ina kake kiwon garkenka kuma ina kake kai tumakinka su huta da tsakar rana. Me ya sa zan kasance kamar macen da aka lulluɓe kusa da garkunan abokanka?8. Ke mafiya kyau a cikin mata, in ba ki sani ba, to, ki dai bi labin da tumaki suke bi ki yi kiwon ’yan awakinki kusa da tentunan makiyaya.9. Ina kwatanta ke ƙaunatacciyata, da goɗiya mai jan keken yaƙin kayan Fir’auna.10. ’Yan kunne sun ƙara wa kumatunki kyau, wuyanki yana da jerin kayan wuya masu daraja.11. Za mu yi ’yan kunnenki na zinariya, da adon azurfa.12. Yayinda sarki yake a teburinsa, turarena ya bazu da ƙanshi.13. Ƙaunataccena yana kamar ƙanshin mur a gare ni, kwance a tsakanin ƙirjina.14. Ƙaunataccena kamar tarin furanni jeji ne gare ni daga gonakin inabin En Gedi.15. Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! Kai, ke kyakkyawa ce! Idanunki kamar na kurciya ne.16. Kai kyakkyawa ne, ƙaunataccena! Kai, kana ɗaukan hankali! Gadonmu koriyar ciyawa ce.17. Al’ul su ne ginshiƙan gidanmu; fir su ne katakan rufin gidanmu.Waƙar Waƙoƙi 2:1-171. Ni furen bi-rana ne na Sharon, furen bi-rana na kwari.2. Kamar furen bi-rana a cikin ƙayayyuwa haka ƙaunatacciyata take a cikin ’yan mata.3. Kamar itacen gawasa a cikin itatuwan jeji haka ƙaunataccena yake a cikin samari. Ina farin ciki in zauna a inuwarsa, ’ya’yan itacensa suna da daɗin ɗanɗanon da nake so4. Ya kai ni babban zauren da ake liyafa, ƙauna ita ce tutarsa a gare ni.5. Ka ƙarfafa ni da zabibi ka wartsake ni da gawasa, gama ina suma don ƙauna.6. Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina, hannunsa na dama kuma ya rungume ni.7. ’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari da bareyi da ƙishimai na jeji. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle.8. Saurara! Ƙaunataccena! Duba! Ga shi ya iso, yana tsalle a duwatsu, yana rawa a bisa tuddai.9. Ƙaunataccena yana kama da barewa ko sagarin ƙishimi Duba! Ga shi can tsaye a bayan katangarmu, yana leƙe ta tagogi, yana kallo ta cikin asabari.10. Ƙaunataccena ya yi magana ya ce mini, “Tashi, ƙaunatacciyata, kyakkyawata, ki zo tare da ni.11. Duba! Damina ta wuce; ruwan sama ya ɗauke ya kuma ƙare.12. Furanni sun hudo a duniya; lokaci yin waƙa ya zo, ana jin kukan kurciyoyi ko’ina a ƙasarmu.13. Itacen ɓaure ya fid da ’ya’yansa da sauri; tohon inabi suna ba da ƙanshinsu. Tashi, zo, ƙaunatacciyata; kyakkyawata, zo tare da ni.”14. Kurciyata a kogon dutse, a wuraren ɓuya a gefen dutse, nuna mini fuskarki, bari in ji muryarki; gama muryarki da daɗi take, fuskarki kuma kyakkyawa ce.15. Kama mana ɓeraye, ƙananan ɓerayen da suke lalatar da gonakin inabi, gonakin inabinmu da suke cikin yin fure.16. Ƙaunataccena nawa ne ni kuma tasa ce; yana kiwon garkensa a cikin furannin bi-rana.17. Sai gari ya waye inuwa kuma ta watse, ka juye, ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko kamar sagarin ƙishimi a kan tuddai masu ciyawa.Zabura 104:1-91. Yabi Ubangiji, ya raina. Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai; kana saye da daraja da ɗaukaka.2. Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga ya shimfiɗa sammai kamar tenti3. ya kafa ginshiƙan ɗakin samansa a kan ruwaye. Ya maido da gizagizai suka zama keken yaƙinsa yana hawa a kan fikafikan iska.4. Ya mai da iska suka zama ’yan saƙonsa harsunan wuta kuma bayinsa.5. Ya kafa duniya a kan tussanta; ba za a iya matsar da ita ba.6. Ka rufe ta da zurfi kamar da riga ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu.7. Amma a tsawatawarka ruwaye suka gudu da jin ƙarar tsawanka suka ruga da gudu;8. suka gudu a bisa duwatsu, suka gangara zuwa cikin kwaruruka, zuwa wurin da ka shirya musu.9. Ka kafa iyakar da ba a iya tsallakawa; ba za su ƙara rufe duniya ba.Karin Magana 24:15-1615. Kada ka kwanta kana fako kamar ɗan iska don ƙwace gidan adali, kada ka ƙwace masa wurin zama;16. gama ko da adali ya fāɗi sau bakwai, yakan tashi kuma, amma bala’i kan kwantar da mugaye.1 Korintiyawa 11:17-3417. Game da umarnan nan dai, ban yaba muku ba, domin taruwarku ba ta kirki ba ce, ɓarna ce.18. Da farko dai, na ji cewa sa’ad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen.19. Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku.20. Sa’ad da kuka taru, ba Cimar Ubangiji kuke ci ba,21. gama yayinda kuke ci, kowa yakan ci gaba ba tare da jiran wani ba. Wani yă zauna da yunwa, wani kuma yă bugu.22. Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? A’a, ko kaɗan!23. Gama abin da na karɓa daga wurin Ubangiji shi ne nake ba ku. Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki burodi,24. bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake dominku, ku yi wannan don tunawa da ni.”25. Haka kuma bayan cimar, ya ɗauki kwaf, yana cewa, “Wannan kwaf ne sabon alkawari a jinina; ku yi wannan, a duk sa’ad da kuke sha, don tunawa da ni.”26. Gama a duk sa’ad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har yă dawo.27. Saboda haka, duk wanda ya ci burodin ko ya sha daga kwaf na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulaƙanta jiki da jinin Ubangiji ke nan.28. Dole kowa yă bincike kansa kafin yă ci burodin yă kuma sha daga kwaf ɗin.29. Gama duk wanda ya ci ya kuma sha ba tare da fahimtar jikin Ubangiji ba, ya ci ya kuma sha wa kansa hukunci ne.30. Shi ya sa da yawa a cikinku ba su da ƙarfi, suna kuma da rashin lafiya, waɗansunku kuma sun riga sun yi barci.31. Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za mu shiga irin hukuncin nan ba.32. Duk da haka sa’ad da Ubangiji ya hukunta mu, ana yin mana horo ne don kada a ƙarshe a hallaka mu tare da duniya.33. Saboda haka ’yan’uwana, sa’ad da kuka taru don ci, ku jira juna.34. In wani yana jin yunwa, sai yă ci abinci a gida, saboda in kuka taru kada yă jawo hukunci. Sa’ad da na zo kuma zan ba da ƙarin umarnai. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.