Baibul a cikin shekara guda Satumba 17Ishaya 25:1-121. Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka, gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki, abubuwan da aka shirya tun da.2. Ka mai da birnin tsibin tarkace, ka lalatar da gari mai katanga, birnin baƙi mai ƙarfi, ta ɓace; ba za a ƙara gina ta ba.3. Saboda haka mutane masu ƙarfi za su girmama ka; biranen mugayen al’ummai za su ji tsoronka.4. Kai ka zama mafakar matalauta, mafaka don mabukata cikin damuwa, wurin ɓuya daga hadari, inuwa kuma daga zafin rana. Gama numfashin mugaye yana kamar da hadari mai bugun bango5. kuma kamar zafin hamada. Ka kwantar da hayaniyar baƙi; kamar yadda inuwar girgije kan rage zafin rana, haka ake kwantar da waƙar mugaye.6. A kan wannan dutse Ubangiji Maɗaukaki zai shirya bikin abinci mai kyau don dukan mutane, liyafar ajiyayyen ruwan inabi da nama mafi kyau da ruwan inabi mafi kyau.7. A wannan dutse zai kawar da baƙin cikin da ya lulluɓe dukan mutane, ƙyallen da ya rufe dukan al’ummai;8. zai haɗiye mutuwa har abada. Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye daga dukan fuskoki; zai kawar da kunyar mutanensa daga dukan duniya. Ubangiji ne ya faɗa.9. A wannan rana za su ce, “Tabbatacce wannan shi ne Allah; mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu. Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi; bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.”10. Hannun Ubangiji zai zauna a kan wannan dutse; amma za a tattake Mowab a ƙarƙashinsa kamar yadda ake tattaka kara a cikin taki.11. Za su buɗe hannuwansa a cikinsa, yadda mai iyo kan buɗe hannuwansa don yă yi iyo. Allah ya ƙasƙantar da girmankansu duk da wayon hannuwansu.12. Zai rurrushe manyan katangar kagaru ya kuma ƙasƙantar da su; zai rushe su har ƙasa, su zama ƙura.Ishaya 26:1-211. A wannan rana za a rera wannan waƙa a ƙasar Yahuda. Muna da birni mai ƙarfi; Allah yake ceton katanga da kuma kagarunta.2. A buɗe ƙofofi saboda al’umma mai adalci ta shiga, al’ummar da mai aminci.3. Za ka kiyaye shi da cikakken salama shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka, domin ya dogara a gare ka.4. Ku dogara ga Ubangiji, gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.5. Yakan ƙasƙantar da waɗanda suke zama a bisa ya kawar da birni mai alfarma ƙasa; ya rusa ta har ƙasa ya jefar da ita cikin ƙura.6. Ƙafafu sukan tattake ta, ƙafafu waɗanda aka zalunta, wato, sawun matalauta.7. Hanyar masu adalci sumul take; Ya Mai Aikata Gaskiya, ka sa hanyar masu adalci ta yi sumul.8. I, Ubangiji, cikin tafiya a hanyar dokokinka, muna sa zuciya gare ka; sunanka da tunani a kanka su ne marmarin zukatanmu.9. Raina yana marmarinka da dare; da safe kuma raina yana son ganinka. Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya, mutanen duniya kan koyi adalci.10. Ko da yake akan nuna wa mugaye alheri, ba sa koyi adalci; har ma a ƙasar masu aikata gaskiya sukan ci gaba da aikata mugunta ba sa ganin girmar darajar Ubangiji.11. Ya Ubangiji an ɗaga hannunka sama, amma ba sa ganinsa. Bari su ga himmarka don mutanenka su kuma sha kunya; bari wutar da aka ajiye don abokan gābanka ta cinye su.12. Ubangiji ka kafa salama dominmu; duk abin da muka iya yi kai ne ka yi mana.13. Ya Ubangiji, Allahnmu, waɗansu iyayengiji ban da kai sun yi mulki a kanmu, amma sunanka kaɗai muka girmama.14. Yanzu duk sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba; waɗannan ruhohin da suka rasu ba za su tashi ba. Ka hukunta su ka kuma kawo su ga hallaka; ka sa ba za a ƙara tunawa da su ba.15. Ka fadada al’umma, ya Ubangiji; ka fadada al’umma. Ka samo wa kanka ɗaukaka; ka fadada dukan iyakokin ƙasar.16. Ubangiji, sun zo gare ka a cikin damuwarsu; sa’ad da ka hore su, da ƙyar suna iya yin addu’a.17. Kamar mace mai ciki da take gab da haihuwa takan yi ta murɗawa tana kuka saboda zafi, haka muka kasance a gabanka, ya Ubangiji.18. Muna da ciki, mun yi ta murɗewa saboda zafi, amma mun haifi iska. Ba mu kawo ceto ga duniya ba; ba mu haifi mutanen duniya ba.19. Amma matattunka za su rayu; jikunansu za su tashi. Ku da kuke zama a ƙura, ku farka ku kuma yi sowa don farin ciki. Raɓarka kamar raɓar safiya ce; duniya za tă haifi matattunta.20. Ku tafi, mutanena, ku shiga ɗakunanku ku kuma kulle ƙofofi; ku ɓoye kanku na ɗan lokaci sai ya huce fushinsa.21. Duba, Ubangiji yana fitowa daga mazauninsa don yă hukunta mutanen duniya saboda zunubansu. Duniya za tă bayyana zub da jinin da aka yi a kanta; ba za tă ƙara ɓoye waɗanda aka kashe a cikinta ba.Zabura 107:23-3223. Waɗansu suka yi tafiya a teku cikin jiragen ruwa; su ’yan kasuwa ne a manyan ruwaye.24. Sun ga ayyukan Ubangiji, ayyukansa masu banmamaki a cikin zurfin teku.25. Gama ya yi magana ya kuma sa iska mai ƙarfi ta tashi ya ɗaga raƙuman ruwa sama.26. Suka hau zuwa sammai suka kuma tsinduma cikin zurfafa; a cikin azabarsu sai ƙarfin halinsu ya karai.27. Suka yi tangaɗi suna tuntuɓe kamar bugaggu; suka kuma kai ga ƙarshen dabararsu.28. Sai suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa fitar da su daga damuwarsu.29. Ya kwantar da hadiri suka yi tsit; raƙuman ruwan teku suka yi shiru.30. Suka yi murna sa’ad da wuri ya kwanta, ya kuma bishe su zuwa inda suka so su kai.31. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.32. Bari su ɗaukaka shi cikin taron mutane su kuma yabe shi cikin taron dattawa.Karin Magana 25:18-1918. Kamar sanda ko takobi ko kibiya mai tsini haka yake da mutumin da yake ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinsa.19. Kamar haƙori mai ciwo ko yin tafiya da gurguwar ƙafa haka yake ga mai dogara da marasa aminci a lokacin wahala.2 Korintiyawa 1:9-159. Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu.10. Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu,11. yayinda kuke taimakonmu ta wurin addu’o’inku. Mutane da yawa kuwa za su yi godiya ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu’o’i masu yawa.12. Wannan shi ne taƙamarmu. Lamirinmu yana ba da shaida cewa mun yi zamanmu a duniya, musamman a dangantakarmu da ku cikin tsarki, tsakani da Allah. Mun yi haka ta wurin bishewar alherin Allah, ba bisa ga hikimar duniya ba.13. Gama ba mu rubuta muku abin da ba za ku iya karatu ko ku kāsa fahimta ba. Ina kuma fata cewa,14. kamar yadda kuka ɗan fahimce mu, za ku kai ga cikakkiyar fahimta cewa za ku iya yin taƙama da mu, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama da ku a ranar da Ubangiji Yesu zai dawo.15. Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.