Baibul a cikin shekara guda Satumba 18Ishaya 27:1-131. A wannan rana, Ubangiji zai yi hukunci da takobi, takobinsa mai tsanani, mai ƙarfi da kuma mai muguwar ɓarna, zai hukunta dodon ruwa macijin nan da ya kanannaɗe, dodon ruwa macijin nan mai murɗewa; zai kashe dodon nan na teku.2. A wannan rana, “Ku rera game da gonar inabi mai ba da ’ya’ya ku ce3. Ni, Ubangiji na lura da ita; na yi ta yin mata banruwa. Na yi tsaronta dare da rana don kada wani yă yi mata ɓarna.4. Ban yi fushi ba. Da a ce ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suke kalubalanta na mana! Zan fita in yi yaƙi da su; da na sa musu wuta duka.5. Ko kuma bari su zo wurina don mafaka; bari su yi sulhu da ni, I, bari su yi sulhu da ni.”6. A kwanaki masu zuwa Yaƙub zai yi saiwa, Isra’ila zai yi toho ya kuma yi fure ya cika dukan duniya da ’ya’ya.7. Ubangiji ya buge shi kamar yadda ya bugi waɗanda suka buge shi? An kashe shi kamar yadda aka kashe waɗanda suka kashe shi?8. Ta wurin yaƙi da zaman bauta ka hukunta shi, da tsananin tsawa kuma ka kore shi, kamar a ranar da iskar gabas ta hura.9. A ta haka fa, za a yi kafarar laifin Yaƙub, wannan kuma zai zama cikakken amfanin kau da zunubinsa. Sa’ad da ya niƙa duwatsun bagade suka zama kamar allin da aka farfashe kucu-kucu, har ba sauran ginshiƙan Ashera ko bagadan ƙona turare da za a bari a tsaye.10. Birni mai katanga ya zama kufai, yasasshen mazauni, an yashe shi kamar hamada; a can ’yan maruƙa suke kiwo, a can suke kwance; sun kakkaɓe rassanta ƙaf.11. Sa’ad da rassanta suka bushe, sai su kakkarye su mata kuma su zo su yi itacen wuta da su. Gama mutane ne marar azanci; saboda haka Mahaliccinsu bai ji tausayinsu ba, Mahaliccinsu bai nuna musu jinƙai ba.12. A wannan rana Ubangiji zai tankaɗe daga Yuferites mai gudu zuwa Rafin Masar, ku kuma, ya Isra’ilawa, za a tattara ku ɗaya-ɗaya.13. Kuma a wannan rana zai busa ƙaho mai kāra sosai. Waɗanda suke mutuwa a Assuriya da kuma waɗanda aka kai zaman bauta a Masar za su zo su kuma yi wa Ubangiji sujada a dutse mai tsarki a Urushalima.Ishaya 28:1-291. Kaito ga wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim, ga fure mai yanƙwanewa, darajar kyansa, da aka sa a kan kwari mai ba da amfani, ga birnin nan, wadda take girman kan waɗanda aka ƙasƙantar da ruwan inabinsu!2. Duba, Ubangiji yana da wanda yake da iko da kuma ƙarfi. Kamar dutsen ƙanƙara da kuma iska mai ɓarna, kamar kwararowar ruwa da rigyawa mai kirmewa, zai jefa shi har ƙasa da ƙarfi.3. Za a tattaka wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim da ƙafa.4. Wannan fure mai yanƙwanewa, darajarar kyansa, da aka sa a kan kwari mai ba da amfani, zai zama kamar ’ya’yan ɓaure, nunan fari, da zarar wani ya gani ya kuma tsinka, zai haɗiye shi.5. A wannan rana Ubangiji Maɗaukaki zai zama rawani mai daraja kyakkyawan rawani wa mutanensa da suka ragu.6. Zai zama ruhun adalci gare shi wanda yake zaune a kujerar shari’a, wurin samun ƙarfi ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofi.7. Da waɗannan kuma masu tangaɗi saboda sun sha ruwan inabi suke jiri don sun sha barasa Firistoci da annabawa suna tangaɗi saboda sun sha barasa sun kuma yi tatur da ruwan inabi; suna jiri saboda sun sha barasa, suna tangaɗi sa’ad da suke ganin wahayi, suna tuntuɓe sa’ad da suke ba da shawara.8. Duk amai ya rufe teburori kuma babu wani wurin da ba a ɓata ba.9. “Wane ne yake so ya koyar? Ga wa yake bayyana saƙonsa? Ga yaran da aka yaye, ga waɗanda ba a daɗe da yayewa ba ne?10. Gama haka yake. Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi, mulki a kan mulki, mulki a kan mulki; nan kaɗan, can kaɗan.”11. To da kyau, da leɓunan baƙi da ku harsunan da ba sani ba Allah zai yi magana da wannan mutane,12. waɗanda zai ce, “Wannan shi ne wurin hutu, bari waɗanda suka gaji su huta”; da kuma, “Wannan shi ne wurin wartsakewa” amma sun ƙi su saurara.13. Saboda haka fa, maganar Ubangiji gare su za tă zama, Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi, mulki akan mulki, mulki a kan mulki; nan kaɗan, can kaɗan, domin su tafi su kuma fāɗi da baya, su ji rauni a kuma kama su da tarko, a kai su zaman bauta.14. Saboda haka ku saurari maganar Ubangiji, ku masu ba’a ku da kuke mulkin wannan mutane a Urushalima.15. Kuna fariya cewa, “Mun yi alkawari da mutuwa, mun kuma yi yarjejjeniya da kabari. Sa’ad da zafi ya ratsa, ba zai taɓa mu ba, gama mun mai da ƙarya mafakarmu ruɗu kuma wurin ɓuyanmu.”16. Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Duba, na kafa dutse a Sihiyona, dutsen da aka gwada, dutsen kusurwa mai daraja don tabbataccen tushe; wanda ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.17. Zan mai da gaskiya igiyar gwaji adalci kuma ɗan katakon gwajin ginin; ƙanƙara za tă share mafakarku, ƙarya, da ruwa kuma za su mamaye maɓuyanku.18. Za a soke alkawarinku da mutuwa; yarjejjeniyarku da kabari ba zai zaunu ba. Sa’ad da zafi mai ɓarna ya ratsa, zai hallaka ku.19. A duk sa’ad da ya zo; ko da safiya, ko dare ko kuma da rana, zai yi ta ratsawa yana kwasanku.” Za ku zama kamar mutumin da ya zama abin karin magana,20. wanda ya yi ƙoƙari yă kwanta a gajeren gado, yă kuma rufa da ɗan siririn bargo.21. Ubangiji zai tashi kamar yadda ya yi a Dutsen Feratsim, zai tā da kansa kamar a Kwarin Gibeyon don yă aikata aikinsa, aikinsa da ba a saba gani ba, yă kuma yi aikinsa, baƙon aikinsa.22. Yanzu ku daina ba’arku, in ba haka ba sarƙoƙinku za su ƙara nauyi; Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa mini game da hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasar.23. Ku saurara ku kuma ji muryata; ku kasa kunne ku kuma ji abin da na faɗa.24. Sa’ad da manomi ya yi noma don shuki, yakan ci gaba da noma ne? Yakan ci gaba da sara yana yin kunyoyi a ƙasa ne?25. Sa’ad da ya shirya wuri da kyau, ba yakan shuka kanumfari ya kuma yayyafa ɗaɗɗoya ba? Ba yakan shuka alkama a kunyoyinsa sha’ir a kunyoyinsa, tamba kuma a filinsa ba?26. Allahnsa ya umarce shi ya kuma koya masa hanyar da take daidai.27. Ba a bugan kanumfari da ƙaton sanda ko a yi ta jujjuye ƙafar keke a kan ɗaɗɗoya; akan buga kanumfari da siririn sanda ɗaɗɗoya kuma da tsumagiya.28. Dole a niƙa hatsi don a yi burodi; saboda haka mutum ba zai yi ta bugun alkama, har yă ɓata tsabar ba. Ya san yadda zai sussuke alkamarsa, ba tare da ya ɓata tsabarta ba.29. Dukan wannan hikimar takan zo daga Ubangiji Maɗaukaki ne, shi da yake mashawarci mai banmamaki, mafifici kuma cikin hikima.Zabura 107:33-4333. Ya mai da koguna suka zama hamada, maɓulɓulai masu gudu suka zama ƙasa mai ƙishirwa,34. ƙasa mai amfani kuma suka zama gishiri marar amfani, saboda muguntar waɗanda suka zauna a can.35. Ya mai da hamada ya zama tafkunan ruwa busasshiyar ƙasa kuma zuwa maɓulɓulai masu gudu;36. a can ya kai mayunwata su yi zama, ya kuma samo birnin da za su zauna.37. Suka yi shuka a gonaki suka dasa inabi suka kuma girbe amfani gona;38. ya albarkace su, yawansu kuma ya ƙaru, bai kuwa bar garkunansu suka ragu ba.39. Sa’an nan yawansu ya ragu, aka kuma ƙasƙantar da su ta wurin danniya, bala’i da kuma baƙin ciki;40. shi da yake kawo reni a kan manyan mutane ya sa suka yi ta yawo a cikin jejin da ba hanya.41. Amma ya fid da mabukata daga wahalarsu ya kuma ƙara iyalansu da tumakinsu.42. Masu yin gaskiya suka gani suka yi farin ciki amma dukan mugaye suka rufe bakunansu.43. Duk mai hikima, bari yă ji waɗannan abubuwa yă kuma lura da ƙauna mai girma ta Ubangiji.Karin Magana 25:20-2020. Kamar wanda ya tuɓe riga a ranar da ake sanyi, ko kuwa kamar zuba ruwan tsami a kanwa, haka yake da mai rera waƙoƙi ga mai baƙin ciki.2 Korintiyawa 10:1-181. Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali’u da sanyin hali na Kiristi, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” a cikinku, amma “mai matsawa” sa’ad da nake rabe da ku!2. Ina roƙonku cewa sa’ad da na zo kada ku tilasta ni in matsa muku, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha’anin duniya ne.3. Ko da yake muna cikin duniya, ba ma yaƙi kamar yadda duniya take yi.4. Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi.5. Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi.6. A shirye muke mu hori kowane rashin biyayya, sa’ad da biyayyarku ta cika.7. Kuna duban abubuwa bisa-bisa ne kawai. In wani ya ganin cewa shi na Kiristi ne, ya kamata yă sāke lura cewa kamar yadda yake na Kiristi, haka mu ma muke.8. Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba ni da abin jin kunya a ciki.9. Ba na so yă zama kamar ina ƙoƙari in tsorata ku ne da wasiƙuna.10. Gama waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa suna da nauyi da kuma ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi, ba shi da wani kwarjini, maganarsa kuma ba kome ba ce.”11. Ya kamata irin waɗannan mutane su gane cewa abin da muke faɗa a cikin wasiƙunmu sa’ad da ba ma nan tare da ku, shi muke aikatawa sa’ad da muke nan.12. Ba za mu yi ƙarfin halin lissafta kanmu, ko mu kwatanta kanmu da waɗansu masu yabon kansu ba. Sa’ad da suke gwada kansu da kansu, da kuma kwatanta kansu da kansu, ba su da hikima.13. Amma mu kam, ba za mu yi taƙama mu zarce iyakarmu ba, sai dai za mu yi taƙama cikin filin da Allah ya ƙayyade mana, filin kuwa ya kai har zuwa wurinku.14. Ba mu wuce gona da iri a taƙamarmu ba, kamar yadda zai zama, da a ce ba mu zo wurinku ba, gama mun kai har wurinku da bisharar Kiristi.15. Fahariyarmu ba fiye da yadda ya kamata take ba, ba tă kuma shafi aikin waɗansu ba. Sai dai muna sa zuciya bangaskiyarku ta riƙa ƙaruwa, ta haka kuma fagen aikinmu a cikinku yă riƙa ƙaruwa ƙwarai da gaske.16. Saboda mu iya yin wa’azin bishara a yankunan da suke gaba da ku. Gama ba ma so mu yi taƙama game da aikin da aka riga aka yi a sashen wani.17. Amma, “Duk mai yin taƙama, sai ya yi taƙama da Ubangiji.”18. Ai, ba mai yabon kansa ake amincewa da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.