Baibul a cikin shekara guda Satumba 21Ishaya 33:1-241. Kaitonka, ya kai mai hallakarwa, kai da ba a hallakar da kai ba! Kaitonka, ya maciya amana, kai da ba a ci amanarka ba! Sa’ad da ka daina hallakarwa, za a hallaka ka; sa’ad da ka daina cin amana, za a ci amanarka.2. Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai; muna marmarinka. Ka zama ƙarfinmu kowace safiya, cetonmu a lokacin damuwa.3. Da tsawar muryarka, mutane za su gudu; sa’ad da ka tashi, al’ummai za su watse.4. Ganimarku, ya al’ummai ƙanana fāri sun girbe; kamar tarin fārin da mutane sun fāɗa wa.5. Ubangiji da girma yake, gama yana zaune a bisa; zai cika Sihiyona cikin gaskiya da adalci.6. Zai zama tabbataccen harsashi na koyaushe, ma’ajin ceto da hikima da sani a yalwace; tsoron Ubangiji shi ne mabuɗin wannan dukiya.7. Duba, jarumawansu suna kuka da ƙarfi a tituna; jakadun salama suna kuka mai zafi.8. An gudu an bar manyan hanyoyi, babu matafiye a kan hanyoyi. Aka keta yarjejjeniya, an rena shaidunsa ba a kuwa ganin girman kowa.9. Ƙasa tana kuka an kuma gudu an bar ta, Lebanon ta sha kunya ta kuma yanƙwane; Sharon ta zama kamar Araba, Bashan da Karmel sun kakkaɓe ganyayensu.10. “Yanzu zan tashi,” in ji Ubangiji. “Yanzu ne za a ɗaukaka ni; yanzu za a ɗaga ni sama.11. Kun yi cikin yayi, kuka haifi kara; numfashinku wuta ne da zai cinye ku.12. Za a ƙone mutane kamar da ƙuna farar ƙasa; kamar ƙayayyuwan da aka sare aka kuma sa musu wuta.”13. Ku da kuke da nesa, ku ji abin da na yi; ku da kuke kusa, ku san ikona!14. Masu zunubi a Sihiyona sun firgita; rawar jiki ya kama marasa sanin Allah suna cewa, “Wane ne a cikinmu zai iya zama da wuta mai ci? Wane ne a cikinmu zai iya zama da madawwamiyar ƙonewa?”15. Shi da yake tafiya cikin adalci yana kuma magana abin da yake daidai, wanda yake ƙin riba daga cuta yana kuma kiyaye hannunsa daga karɓan cin hanci, wanda yake hana kunnuwansa daga ƙulla kisa ya kuma rufe idanunsa a kan tunanin aikata mugunta,16. shi ne mutumin da zai zauna a bisa, wanda mafakarsa za tă zama kagarar dutse. Za a tanada abincinsa, kuma ruwa ba zai kāsa masa ba.17. Idanunku za su ga sarki a cikin kyansa ku kuma hangi ƙasar da take shimfiɗe can da nisa.18. Cikin tunaninku za ku yi tunani firgitar da ta faru tun dā kuna cewa, “Ina hafsan nan? Ina wannan wanda yake karɓar haraji? Ina hafsan da yake lura da hasumiyoyi?”19. Ba za ku ƙara ganin waɗannan mutane masu girman kai kuma ba, waɗannan mutane masu magana da harshen da ba ku fahimta ba.20. Ku duba Sihiyona, birnin shagulgulanmu; idanunku za su ga Urushalima, mazauni mai lafiya, tentin da ba za a taɓa gusar ba; wanda ba a taɓa tumɓuke turakunsa ba, ko a tsinke igiyoyinta.21. A can Ubangiji zai zama Mai Iko Duka namu. Zai zama kamar inda manyan koguna da rafuffuka suke. Matuƙan jirgin ruwa ba za su kai wurinsu ba, manyan jiragen ruwa ba za su yi zirga-zirga a kansu ba.22. Gama Ubangiji ne alƙalinmu, Ubangiji ne mai ba mu dokoki, Ubangiji ne sarkinmu; shi ne wanda zai cece mu.23. Maɗaurinku sun kunce ƙarfafan itacen jirgin ba su da kāriya, fikafikan jirgin ba su buɗu ba. Ta haka za a raba yalwar ganima har ma guragu za su kwashe ganimar.24. Ba wani mazauna a Sihiyona da zai ce, “Ina ciwo”; za a kuma gafarta zunuban waɗanda suke zama a can.Ishaya 34:1-171. Ku zo kusa, ku al’ummai, ku kuwa saurara ku kasa kunne, ku mutane! Bari duniya ta ji, da kuma dukan abin da yake cikinta, duniya, da dukan abin da yake fitowa daga gare ta!2. Ubangiji yana fushi da dukan al’ummai; hasalarsa tana a kan mayaƙansu. Zai hallaka su tas, zai ba da su a karkashe.3. Za a jefar da waɗanda aka kashe gawawwakinsu za su yi wari; duwatsu za su jiƙu da jininsu.4. Za a tumɓuke dukan taurarin sammai za a kuma nannaɗe sararin sama kamar littafi; dukan rundunar sama za su fāffāɗi kamar ganyayen da suka yanƙwane daga kuringa, kamar ’ya’yan ɓauren da suka bushe daga itacen ɓaure.5. Takobina ya sha zararsa a cikin sammai; duba, ya sauko cikin hukunci a kan Edom, mutanen da zan hallaka tas.6. Takobin Ubangiji ya jiƙu da jini, ya rufu da kitse, jinin raguna da na awaki, kitse daga ƙodar raguna. Gama Ubangiji ya yi hadayar Bozra da kuma babban kisa a Edom.7. Babban bijimin jeji zai fāɗi tare da su, maruƙan bijimi da manyan bijimai. Ƙasarsu za tă cika da jini, ƙura kuma zai cika da kitse.8. Gama Ubangiji yana da ranar ɗaukar fansa, shekarar ramuwa, don biya wa Sihiyona bukata.9. Za a mai da rafuffukan Edom rami, ƙurarta za tă zama kibiritun farar wuta; ƙasarta za tă zama rami mai ƙuna!10. Ba za a kashe ta ba dare da rana; hayaƙinta za tă yi ta tashi har abada. Daga tsara zuwa tsara za tă zama kango; babu wani da zai ƙara wucewa ta wurin.11. Mujiyar hamada da mujiya mai kuka za su mallake ta; babban mujiya da hankaka za su yi sheƙa a can. Allah zai miƙe a kan Edom magwajin bala’i da ma’aunin kango.12. Sarakunanta ba za su kasance da wani abin da ake kira masarauta ba, dukan sarakunanta za su ɓace.13. Ƙayayuwa za su mamaye fadodinta ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za su cika kagaranta. Za tă zama mazaunin diloli da gida don mujiyoyi.14. Halittun hamada za su sadu da kuraye, awakin jeji za su yi ta kiran juna; a can halittun dare su ma za su huta su kuma nemi wurin hutu wa kansu.15. Mujiya za tă yi sheƙa a can ta zuba ƙwai; za tă ƙyanƙyashe su, ta kuma kula da ’ya’yanta a inuwar fikafikanta; a can kuma shirwa za su taru, kowa da abokinsa.16. Duba a cikin littafin Ubangiji ka kuma karanta. Babu wani a cikin waɗannan da ya ɓace, babu ko ɗaya da ba ta da abokiya. Gama bakinsa ne ya ba da umarni, Ruhunsa kuma zai tara su wuri ɗaya.17. Ya ba su rabonsu; hannunsa ya rarraba musu ta wurin awo. Za su mallake ta har abada su kuma zauna a can daga tsara zuwa tsara.Zabura 109:1-51. Ya Allah, wanda nake yabo, kada ka yi shiru,2. gama mugaye da masu ruɗu sun buɗe bakunansu a kaina; sun yi magana a kaina da harsunan ƙarya.3. Da kalmomin ƙiyayya sun kewaye ni; sun tasar mini ba dalili.4. A maimakon ƙauna sun sāka mini da zargi, amma ni mutum ne mai addu’a.5. Sun sāka mini alheri da mugunta, ƙauna kuma da ƙiyayya.Karin Magana 25:25-2625. Kamar ruwan sanyi ga ran da ya gaji haka yake da jin labari mai daɗi daga ƙasa mai nisa.26. Kamar rafi mai laka ko rijiyar da ta gurɓace haka yake da mai adalci wanda ya miƙa wuya ga mugaye.2 Korintiyawa 12:1-211. Dole in ci gaba da yin taƙama. Ko da yake ba za tă amfane ni ba, zan yi magana a kan ru’uyoyi da wahayoyi waɗanda na karɓa daga Ubangiji.2. Na san wani a cikin Kiristi wanda shekaru goma sha huɗu da suka wuce an ɗauke zuwa sama ta uku. Ko a cikin jiki ne, ko kuwa ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, Allah ne ya sani.3. Na kuma san cewa wannan mutum, ko a cikin jiki ne, ko kuma ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, amma Allah ne ya sani,4. an ɗauke shi ne zuwa aljanna. Ya ji waɗansu abubuwa waɗanda ba zai iya faɗarsu da kalmomi ba, abubuwan da ba a ba wa mutum damar faɗi.5. Zan yi taƙama game da mutum irin wannan, sai dai ni ba zan yi taƙama da kaina ba, sai dai a kan rashin ƙarfina.6. Ko da zan so yin gadara ma, ba zan zama wawa ba, gama gaskiya zan faɗa. Amma na bar zancen haka, don kada wani ya ɗauke ni fiye da yadda yake ganina, ko yadda yake jin maganata.7. Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni.8. Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu.9. Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni.10. Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.11. Na yi wauta kam, amma ku ne kuke tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini, domin ba inda na kāsa waɗannan mafiffitan manzanni, ko da yake ni ba kome ba ne.12. Abubuwan da suke tabbatar da manzo, alamu, abubuwa da kuma ayyukan banmamaki, an aikata su a cikinku da matuƙar nacewa.13. Ta yaya ne darajarku ba tă kai ta sauran ikkilisiyoyi ba, ko kuwa don dai ban nawaita muku ba ne? Ku gafarta mini wannan laifi!14. Yanzu a shirye nake in ziyarce ku sau na uku, ba zan kuma nawaita muku ba, don ba kayanku nake so ba, ku nake so. Gama ba yara ne da ɗaukar nauyin iyayensu ba, sai dai iyaye ne da ɗaukar nauyin yaran.15. Don haka ina farin ciki in kashe dukan abin da nake da shi a kanku, har in ba da kaina ma dominku. In na ƙaunace ku fiye da haka, za ku rage ƙaunarku gare ni ne?16. To, shi ke nan, ban nawaita muku ba. Ashe, sai ku ce dabara na yi muku, na shawo kanku ta hanyar yaudara!17. Na cuce ku ne ta wurin wani daga cikin waɗanda na aiko a gare ku?18. Na roƙi Titus ya zo wurinku. Na kuma aiki ɗan’uwanmu tare da shi. Ko Titus ya cuce ku ne? Ba ruhu ɗaya yake bi da mu ba? Ba kuma hanya guda muka bi ba?19. Ko tun dā can, kuna tsammani muna kāre kanmu a gare ku ne? A gaban Allah muke magana, kamar waɗanda suke cikin Kiristi. Ƙaunatattuna, kome da muke yi, muna yi ne don inganta ku ne.20. Gama ina tsoro, in na zo, in tarar da ku dabam da yadda nake so, ku ma ku tarar da ni dabam da yadda kuke so. Ina tsoro kada yă zama akwai faɗa, da kishi, da fushi mai zafi, da tsattsaguwa, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da hargitsi.21. Ina tsoro kada sa’ad da na sāke zuwa, Allahna zai ƙasƙantar da ni a gabanku, kuma in yi baƙin ciki saboda waɗanda suka yi zunubi a dā, ba su kuma tuba daga aikin ƙazanta, da na fasikanci, da kuma lalata da suka sa kansu a ciki ba. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.