Baibul a cikin shekara guda Satumba 23Ishaya 37:1-381. Sa’ad da Sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakkece rigunansa ya kuma sanya tsummoki ya tafi ya shiga haikalin Ubangiji.2. Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna magatakarda da kuma manyan firistoci, duka sanye da tsummoki, wurin Ishaya ɗan Amoz.3. Suka faɗa masa cewa, “Ga abin da Hezekiya ya ce wannan rana ce ta baƙin ciki da tsawatawa da shan kunya, sai ka ce sa’ad da ’ya’ya kan zo matakin haihuwa sa’an nan a rasa ƙarfin haihuwarsu.4. Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka zai ji maganganun sarkin yaƙin da maigidansa, sarkin Assuriya, ya aika don yă zagi Allah mai rai, ya kuma tsawata masa saboda maganganun da Ubangiji Allahnka ya ji. Saboda haka ka yi addu’a saboda raguwar da suke da rai.”5. Sa’ad da shugabannin Sarki Hezekiya suka zo wurin Ishaya,6. sai Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku cewa, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa. Kada ka ji tsoron abin da ka ji, maganganun nan da bayin sarkin Assuriya suka yi mini saɓo.7. Ka saurara! Zan sa ruhuna a cikinsa saboda sa’ad da ya ji wani labari, zai koma zuwa ƙasarsa, a can kuwa zan sa a kashe shi da takobi.’ ”8. Sa’ad da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye ya kuma sami sarki yana yaƙi da Libna.9. To, fa, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana fitowa don yă yi yaƙi da shi. Sa’ad da ya ji haka, sai ya aiki jakadu zuwa wurin Hezekiya da wannan magana.10. “Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda cewa kada ka bar allahn da ka dogara a kai ya ruɗe ka sa’ad da ya ce, ‘Ba za a ba da Urushalima ga sarkin Assuriya ba.’11. Tabbatacce ka ji abin da sarakunan Assuriya suka aikata ga dukan ƙasashe, suna hallaka su tas. Kai kuwa za ka tsira ne?12. Allolin al’umman da kakannina suka hallaka sun cece su ne, allolin Gozan, Haran, Rezef da kuma na mutanen Eden waɗanda suke zama a Tel Assar?13. Ina sarkin Hamat yake, sarkin Arfad fa, sarkin Sefarfayim, ko na Hena ko na Iffa?”14. Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga jakadun ya karanta ta. Sa’an nan ya haura zuwa haikalin Ubangiji ya shimfiɗa ta a gaban Ubangiji.15. Sai Hezekiya ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce,16. “Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, zaune a tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah a kan dukan masarautan duniya.17. Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka kuma ji; ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka kuma gani; ka saurara ga dukan maganganun da Sennakerib ya aika don yă zagi Allah mai rai.18. “Gaskiya ce, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriyawa sun mai da dukan waɗannan mutane da ƙasashensu kango.19. Sun jefar da gumakansu cikin wuta suka kuma hallaka su, gama su ba alloli ba ne itace ne kawai da dutse, da hannuwan mutane suka sarrafa.20. Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, saboda masarautai a duniya su san cewa kai kaɗai ne, ya Ubangiji, Allah.”21. Sa’an nan Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo wa Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa. Saboda ka yi addu’a gare ni game da Sennakerib sarkin Assuriya,22. ga abin da maganar Ubangiji ya faɗa a kansa, “Budurwa Diyar Sihiyona ta rena tana kuma maka ba’a. Diyar Urushalima tana kada kai yayinda kake gudu.23. Wane ne ka zargi ka kuma yi wa saɓo? A kan wa ka tā da muryarka ka kuma daga idanu cikin fariya? A kan Mai Tsarkin nan na Isra’ila!24. Ta wurin jakadunka ka jibge zage-zage a kan Ubangiji. Ka kuma ce, ‘Da kekunan yaƙina masu yawa na hau ƙwanƙolin duwatsu, ƙwanƙolin mafi tsayi na Lebanon. Na sassare al’ul mafi tsayi fir mafi kyau. Na kai can wuri mafi nisa na kurminsa.25. Na haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa na kuma sha ruwa a can. Da tafin ƙafafuna na busar da dukan rafuffukan Masar.’26. “Ba ka ji ba cewa tun dā can na shirya ya zama haka? A kwanakin dā na kafa shi; yanzu na sa ya faru, cewa ka mai da birane masu mafaka zuwa tsibin ɓuraguzai.27. Mutanensu, suka rasa ƙarfi, sun firgita suka kuma sha kunya. Suka zama kamar tsire-tsire a gona, kamar tsire-tsiren ta suka tohu, kamar ciyawar da ya tsiro a kan rufi, wadda zafi ya yi wa ƙuna kafin tă yi girma.28. “Amma na san inda kake zama da sa’ad da kakan fita ka kuma koma da yadda ka harzuƙa gāba da ni.29. Saboda ka harzuƙa gāba da ni kuma saboda girmankanka ya kai kunnuwana, zan sa ƙugiya a hancinka linzamina a bakinka, zan kuma sa ka koma ta hanyar da ka zo.30. “Wannan zai zama alama gare ka, ya Hezekiya, “Wannan shekara za ka ci abin da ya yi girma da kansa, shekara ta biyu kuma abin da ya tsiro daga wancan. Amma a shekara ta uku za ka yi shuki ka kuma girba, za ka dasa gonakin inabi ka kuma ci ’ya’yansu.31. Sauran da suka rage na gidan Yahuda kuwa za su yi saiwa a ƙarƙashi su kuma ba da ’ya’ya a bisa.32. Gama daga Urushalima raguwa za tă fito, kuma daga Dutsen Sihiyona ƙungiyar waɗanda suka tsira. Himmar Ubangiji Maɗaukaki zai cika wannan.33. “Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarkin Assuriya, “Ba zai shiga wannan birni ba ya harbe kibiya a nan. Ba zai zo gabansa da garkuwa ba ko ya gina mahaurai kewaye a kansa ba.34. Ta hanyar da ya zo da ita zai koma; ba zai shiga wannan birni ba,” in ji Ubangiji.35. “Zan kāre wannan birni in kuma cece shi, saboda girmana da kuma saboda sunan Dawuda bawana!”36. Sai mala’ikan Ubangiji ya fita ya kuma karkashe mutane dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar a sansanin Assuriya. Sa’ad da mutane suka farka kashegari, sai ga gawawwaki duk a kwance!37. Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya janye. Ya koma zuwa Ninebe ya zauna a can.38. Wata rana, yayinda yake yin sujada a haikalin allahnsa Nisrok, ’ya’yansa maza Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka kuma gudu zuwa ƙasar Ararat. Esar-Haddon ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.Ishaya 38:1-221. A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da ciwo ya kuma kusa ya mutu. Annabi Ishaya ɗan Amoz ya tafi wurinsa ya kuma ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce ka shirya gidanka, domin za ka mutu; ba za ka warke ba.”2. Hezekiya ya juye fuskarsa wajen bango ya kuma yi addu’a ga Ubangiji,3. “Ka tuna, ya Ubangiji, yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da dukan zuciya na kuma yi abin da yake nagari a idanunka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi.4. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Ishaya cewa,5. “Ka tafi ka faɗa wa Hezekiya, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, ya ce na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan ƙara maka shekaru goma sha biyar ga rayuwarka.6. Zan kuwa cece ka da wannan birni daga hannun sarkin Assuriya. Zan kiyaye wannan birni.7. “ ‘Ga alamar Ubangiji gare ka cewa Ubangiji zai aikata kamar yadda ya yi alkawari.8. Zan sa inuwar da rana ta yi a kan matakalar Ahaz ta koma baya da taki goma.’ ” Saboda haka inuwar ta koma da baya daga fuskar rana har taki goma.9. Rubutun Hezekiya sarkin Yahuda bayan ciwonsa da kuma warkarwarsa.10. Na ce, “Cikin tsakiyar rayuwata dole in bi ta ƙofofin mutuwa a kuma raba ni da sauran shekaruna?”11. Na ce, “Ba zan ƙara ganin Ubangiji ba, Ubangiji a ƙasa ta masu rai; ba zan ƙara ga wani mutum, ko in kasance tare da waɗanda suke zama a wannan duniya ba.12. Kamar tentin makiyayi an rushe gidana aka kuma ƙwace ta daga gare ni. Kamar mai saƙa, na nannaɗe rayuwata, ya kuma yanke ni daga sandar saƙa; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.13. Na yi jira da haƙuri har safiya, amma kamar zaki ya kakkarya ƙasusuwana duka; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.14. Na yi kuka kamar mashirare ko zalɓe, na yi kuka kamar kurciya mai makoki. Idanuna suka rasa ƙarfi yayinda na duba sammai. Na damu; Ya Ubangiji, ka taimake ni!”15. Amma me zan ce? Ya riga ya yi mini magana, shi kansa ne kuma ya aikata. Zan yi tafiya da tawali’u dukan kwanakina saboda wahalar raina.16. Ubangiji, ta waɗannan abubuwa ne mutane suke rayuwa; ruhuna kuma yana samun rai a cikinsu shi ma. Ka maido mini da lafiya ka kuma sa na rayu.17. Tabbatacce wannan kuwa saboda ribata ne cewa in sha irin wahalan nan. Cikin ƙaunarka ka kiyaye ni daga ramin hallaka; ka sa dukan zunubaina a bayanka.18. Gama kabari ba zai yabe ka ba, matattu ba za su rera yabonka ba; waɗanda suka gangara zuwa rami ba za su sa zuciya ga amincinka ba.19. Masu rai, masu rai, su suke yabonka, kamar yadda nake yi a yau; iyaye za su faɗa wa ’ya’yansu game da amincinka.20. Ubangiji zai cece ni, za mu kuma rera da kayan kiɗi masu tsirkiya dukan kwanakinmu a cikin haikalin Ubangiji.21. Ishaya ya riga ya ce, “Ku shirya curin da aka yi da ’ya’yan ɓaure ku kuma shafa a marurun, zai kuwa warke.”22. Hezekiya ya riga ya yi tambaya ya ce, “Me zai zama alama ta cewa zan haura zuwa haikalin Ubangiji?”Zabura 109:14-2014. Bari a tuna da laifin kakanninsa a gaban Ubangiji; bari kada a taɓa shafe zunubin mahaifiyarsa.15. Bari zunubansu su kasance a gaban Ubangiji kullum, don yă sa a manta da su daga duniya.16. Gama bai taɓa yin tunanin yin alheri ba, amma ya tsananta wa matalauta da mabukata da kuma masu fid da zuciya har suka mutu.17. Yana jin daɗin la’antarwa, bari yă dawo a kansa; ba ya son sa albarka, bari kada kowa yă sa masa albarka.18. Ya sa la’antarwa kamar rigarsa; ta shiga cikin jikinsa kamar ruwa, cikin ƙasusuwansa kamar mai.19. Bari tă zama kamar mayafin da aka ɗaura kewaye da shi, kamar ɗamara da aka ɗaura kewaye da shi har abada.20. Bari wannan yă zama sakayyar Ubangiji ga masu zargina, ga waɗanda suke mugayen maganganu a kaina.Karin Magana 26:1-11. Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi, haka girmamawa bai dace da wawa ba.Galatiyawa 1:1-241. Bulus manzo, aikakke ba daga wurin mutum ba, ba kuma ta wurin mutane ba, amma ta wurin Yesu Kiristi da kuma Allah Uba, wanda ya tā da Yesu daga matattu.2. Dukan ’yan’uwan kuma da suke tare da ni a nan, Suna gai da ikkilisiyoyi a Galatiya.3. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.4. Shi wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu don yă cece mu daga wannan mugun zamani na yanzu, bisa ga nufin Allah wanda yake kuma Ubanmu,5. a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.6. Ina mamaki yadda kuka yi saurin yashe wanda ya kira ku ta wurin alherin Kiristi, kuna juyewa ga wata bishara dabam7. wadda a gaskiya ba bishara ba ce ko kaɗan. Tabbatacce waɗansu mutane suna birkitar da ku, suna kuma ƙoƙari su karkatar da bisharar Kiristi.8. Amma ko mu, ko mala’ika daga sama ya yi wa’azin wata bishara dabam da wadda muka yi muku, bari yă zama la’ananne har abada!9. Kamar yadda muka riga muka faɗa, haka yanzu ma ina ƙara cewa in wani yana muku wa’azin wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, bari yă zama la’ananne har abada!10. Za a ce, ina ƙoƙarin neman amincewar mutane ne, ko amincewa ta Allah? Ko kuwa ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne? Da a ce har yanzu ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne, ai, da ban zama bawan Kiristi ba.11. Ina so ku sani ’yan’uwa, cewa bisharar da nake wa’azi, ba mutum ne ya ƙago ta ba.12. Ban karɓe ta daga wurin wani mutum ba, ba a kuma koya mini ita ba, a maimako, na karɓe ta, ta wurin wahayi daga Yesu Kiristi ne.13. Kun dai ji labarin rayuwata ta dā a cikin Yahudanci, yadda na tsananta wa ikkilisiyar Allah ƙwarai, na kuma yi ƙoƙarin hallaka ta.14. Na ci gaba a cikin Yahudanci fiye da yawancin Yahudawan da suke tsarana, na kuma yi ƙwazo ƙwarai ga bin al’adun kakannina.15. Amma sa’ad da Allah, wanda ya keɓe ni daga mahaifa ya kira ni ta wurin alherinsa, ya kuma gamshe shi16. yă bayyana Ɗansa a cikina, domin in yi wa’azinsa cikin Al’ummai. Ban nemi shawarar wani mutum ba.17. Ban kuma tafi Urushalima domin in ga waɗanda suka riga ni zaman manzanni ba, sai dai na hanzarta na tafi ƙasar Arabiya, daga baya sai na koma Damaskus.18. Bayan shekara uku, sai na haura zuwa Urushalima domin in sadu da Bitrus, na kuwa zauna tare da shi kwana goma sha biyar.19. Ban ga wani a ciki sauran manzanni ba, sai dai Yaƙub ɗan’uwan Ubangiji.20. Ina tabbatar muku a gaban Allah cewa abin da nake rubuta muku ba ƙarya ba ne.21. Daga baya sai na tafi Suriya da Silisiya.22. Ikkilisiyoyin da suke cikin Kiristi da suke a Yahudiya ba su san ni ba tukuna.23. Sun dai sami labari ne kawai cewa, “Mutumin da dā yake tsananta mana yanzu yana wa’azin bangaskiyar da dā ya yi ƙoƙari yă hallaka.”24. Sai suka yabi Allah saboda ni. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.