Baibul a cikin shekara guda Satumba 24Ishaya 39:1-81. A wannan lokaci Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu da kuma kyauta, domin ya ji rashin lafiyarsa da kuma warkarwarsa.2. Hezekiya ya marabci jakadun da murna ya kuma nuna musu abin da gidajen ajiyarsa sun ƙunsa, azurfa, zinariya, yaji, tatsatsen mai, dukan kayan yaƙinsa da kuma kome da yake a ma’ajinsa. Babu abin da yake a cikin fadansa ko cikin dukan masarautarsa da Hezekiya bai nuna musu ba.3. Sai Ishaya annabi ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya kuma tambaye shi ya ce, “Mene ne waɗannan mutane suka faɗa, kuma daga ina suka fito?” Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Sun zo ne daga Babilon.”4. Annabi ya yi tambaya ya ce, “Mene ne suka gani a fadanka?” Hezekiya ya ce, “Sun ga kome da kome a fadana. Babu abin da ban nuna musu a cikin ma’ajina ba.”5. Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji maganar Ubangiji Maɗaukaki.6. Tabbatacce lokaci yana zuwa sa’ad da kome da yake cikin fadanka, da kuma dukan abin da kakanninka suka ajiye har yă zuwa yau, za a kwashe zuwa Babilon babu abin da za a bari, in ji Ubangiji.7. Waɗansu cikin zuriyarka, nama da jininka waɗanda za a haifa maka, za a kwashe su a tafi, za su zama bābānni a fadan sarkin Babilon.”8. Hezekiya ya ce, “Maganar Ubangiji da ka yi tana da kyau.” Gama ya yi tunani a ransa cewa, “Salama da kāriya za su kasance a zamanina.”Ishaya 40:1-311. Ta’aziyya, ku ta’azantu mutanena, in ji Allahnku.2. Yi magana mai kwantar da rai ga Urushalima, ku kuma furta mata cewa aiki mai zafinta ya isa, cewa an fanshi zunubinta, cewa ta karɓi daga hannun Ubangiji ninki biyu saboda dukan zunubanta.3. Muryar wani tana kira cewa, “A cikin hamada ku shirya hanya saboda Ubangiji; ku miƙe manyan hanyoyi domin Allahnmu a cikin jeji.4. Za a cike kowane kwari, a baje kowane dutse da kowane tudu; za a mayar da karkatattun wurare su zama sumul, munanan wurare kuma su zama da kyau.5. Za a kuma bayyana ɗaukakar Ubangiji, dukan mutane kuwa za su gan ta. Gama Ubangiji da kansa ne ya yi magana.”6. Muryar tana cewa, “Ka yi shela.” Na kuwa ce, “Me zan yi shelar?” “Dukan mutane kamar ciyawa suke, kuma dukan ɗaukakarsu kamar furannin jeji ne.7. Ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi, domin Ubangiji ya hura iska a kansu. Tabbatacce mutane ciyawa ne.8. Hakika ciyawa takan yanƙwane, furanni kuma su yi yaushi, amma maganar Allahnmu tana nan daram har abada.”9. Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Sihiyona, ka haura a bisa dutse. Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Urushalima, ka tā da muryarka ka yi ihu, ka ɗaga ta, kada ka ji tsoro; faɗa wa garuruwan Yahuda, “Ga Allahnku!”10. Duba, Ubangiji Mai Iko Duka yana zuwa da iko, hannunsa kuma yana yin mulki dominsa. Duba, ladarsa tana tare da shi, sakamakonsa kuma na rakiyarsa.11. Yakan lura da garkensa kamar makiyayi. Yakan tattara tumaki wuri ɗaya yă riƙe su kurkusa da ƙirjinsa; a hankali kuma yakan bi da masu ba da mama.12. Wane ne ya auna ruwaye a tafin hannunsa, ko kuwa ya gwada tsawon sammai da fāɗin tafin hannunsa? Wane ne ya riƙe ƙurar ƙasa a kwando, ko kuwa ya auna nauyin duwatsu a magwaji, tuddai kuma a ma’auni?13. Wane ne ya fahimci zuciyar Ubangiji, ko kuwa ya koya masa a matsayin mashawarcinsa?14. Wane ne Ubangiji ya nemi shawararsa don yă ganar da shi, wane ne kuma ya koya masa hanyar da ta dace? Wane ne ya koya masa sani ko ya nuna masa hanyar fahimta?15. Tabbatacce al’ummai suna kama da ɗigon ruwa a cikin bokiti an ɗauke su a matsayin ƙura a kan magwaji; yakan auna tsibirai sai ka ce ƙura mai laushi.16. Itatuwan Lebanon ba su isa a yi wutar bagade da su ba, balle dabbobinsa su isa yin hadayun ƙonawa.17. A gabansa dukan al’ummai ba kome ba ne; ya ɗauke su ba a bakin kome ba kuma banza ne kurum.18. To, ga wane ne za ka kwatanta Allah? Wace siffa za ka kwatanta shi da ita?19. Gunki dai, maƙeri kan yi zubinsa, maƙerin zinariya kuma yă ƙera shi da zinariya yă kuma sarrafa masa sarƙoƙin azurfa.20. Mutumin da talauci ya sha kansa da ba zai iya miƙa irin hadayar nan ba kan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba. Yakan nemi gwanin sassaƙa don yă sassaƙa masa gunkin da ba zai fāɗi ba.21. Ba ku sani ba? Ba ku taɓa ji ba? Ba a faɗa muku daga farko ba? Ba ku fahimta ba tun kafawar duniya?22. Yana zaune a kursiyi a bisa iyakar duniya, kuma mutanenta suna kama da fāra. Ya miƙa sammai kamar rumfa, ya kuma shimfiɗa su kamar tentin da za a zauna a ciki.23. Yakan mai da sarakuna ba kome ba yă mai da masu mulkin wannan duniya wofi.24. Ba da jimawa ba bayan an shuka su, ba da jimawa ba bayan an dasa su, ba da jimawa ba bayan sun yi saiwa a ƙasa, sai yă hura musu iska su yanƙwane, guguwa kuma ta kwashe su kamar yayi.25. “Ga wa za ku kwatanta ni? Ko kuwa wa yake daidai da ni?” In ji Mai Tsarkin nan.26. Ku ɗaga idanunku ku duba sammai. Wane ne ya halicce dukan waɗannan? Wane ne ya fitar da rundunar taurari ɗaya-ɗaya, yana kiransu, kowanne da sunansa. Saboda ikonsa mai girma da kuma ƙarfinsa mai girma, babu ko ɗayansu da ya ɓace.27. Ya Yaƙub, ya Isra’ila, me ya sa kake ce kana kuma gunaguni cewa, “Hanyata tana a ɓoye daga Ubangiji; Allah bai kula da abin da yake damuna ba”?28. Ba ku sani ba? Ba ku ji ba? Ubangiji madawwamin Allah ne, Mahaliccin iyakokin duniya. Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba, kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.29. Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.30. Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala, samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;31. amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji za su sabunta ƙarfinsu. Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa; za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba, za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.Zabura 109:21-2521. Amma kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi da ni da kyau saboda sunanka; ta alherin ƙaunarka, ka cece ni.22. Gama ni matalauci ne mai bukata kuma, zuciyata kuwa ta yi rauni a cikina.23. Na ɓace kamar inuwar yamma; ana kakkaɓe ni kamar fāra.24. Gwiwoyina suna mutuwa saboda azumi; jikina ya rame ba kuma ƙarfi.25. Na zama abin dariya ga masu zargina; sa’ad da suka gan ni, suka kaɗa kawunansu.Karin Magana 26:2-22. Kamar gwara mai yawo ko alallaka mai firiya, haka yake da la’anar da ba tă dace tă kama ka ba take.Galatiyawa 2:1-211. Bayan shekara goma sha huɗu sai na sāke haurawa zuwa Urushalima, a wannan lokaci na tafi tare da Barnabas. Na kuma ɗauki Titus muka tafi tare.2. Na tafi ne bisa ga wani wahayi. Da na kai can, sai na bayyana musu bisharar da nake wa’azi a cikin Al’ummai. Na yi haka a keɓance a gaban waɗanda suke shugabanni, don tsoro kada gudun da nake yi, ko kuwa na riga na yi, yă zama a banza.3. Amma ko Titus ma da yake tare da ni, ba a ce dole sai ya yi kaciya ba, ko da yake shi mutumin Al’ummai ne.4. Wannan zancen kaciya ya taso domin waɗansu ’yan’uwan ƙarya sun shiga cikinmu domin su yi leƙe a kan ’yancin da muke da shi a cikin Kiristi Yesu, su kuma mai da mu bayi.5. Ba mu kuwa ba su zarafi ba ko kaɗan, don gaskiyar bishara ta ci gaba da kasance tare da ku.6. Game da waɗanda aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne, ko wane ne su, duk ɗaya ne a wurina; gama Allah ba ya nuna bambanci, ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙara mini kome ba.7. A maimakon haka, sun ga cewa an danƙa mini hakkin wa’azin bishara ga Al’ummai, kamar yadda aka danƙa wa Bitrus ga Yahudawa.8. Gama Allah wanda ya yi aiki a cikin hidimar Bitrus a matsayin manzo ga Yahudawa, haka ma ya yi aiki a cikin hidimata a matsayin manzo ga Al’ummai.9. Yaƙub, Bitrus da Yohanna waɗanda suke fitattun ginshiƙai, sun karɓe ni da Barnabas da hannu biyu biyu sa’ad da suka gane alherin da aka ba ni. Suka kuma yarda cewa ya kamata mu tafi wajen Al’ummai, su kuwa su tafi wajen Yahudawa.10. Abin da dai suka roƙa shi ne ya kamata mu riƙa tuna da matalauta, abin nan da nake marmarin yi.11. Sa’ad da Bitrus ya zo Antiyok, na tsawata masa ido da ido don laifinsa a fili yake.12. Kafin waɗansu mutane su zo daga wurin Yaƙub, yakan ci abinci tare da Al’ummai. Amma da suka iso, sai ya fara janyewa, ya kuma ware kansa daga wajen Al’ummai domin yana tsoron waɗanda suke ƙungiyar masu kaciya.13. Sauran Yahudawa suka haɗa kai da shi a munafuncinsa har Barnabas ma ya bauɗe.14. Da na ga cewa ba sa yin daidai da gaskiyar bishara, sai na ce wa Bitrus a gabansu duka, “Kai mutumin Yahuda ne, duk da haka kana rayuwa kamar Ba’al’umme ba kamar mutumin Yahuda ba. To, yaya aka yi, kana tilasta Al’ummai su bi al’adun Yahudawa?15. “Mu da muke Yahudawa ta wurin haihuwa ba Al’ummai masu zunubi ba,16. mun san cewa mutum ba ya samun kuɓuta ta wurin kiyaye Doka, sai dai ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Saboda haka, mu ma, muka sa bangaskiyarmu cikin Kiristi Yesu don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya cikin Kiristi ba ta wurin kiyaye Doka ba, domin ba wanda zai kuɓuta ta wurin bin Doka.17. “In kuwa ya zama muna so mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Kiristi, sa’an nan an same mu mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, ko wannan zai nuna Kiristi yana ƙarfafa zunubi ke nan? A’a, ko kusa!18. In na sāke gina abin da na rushe, na zama mai karyar Doka ke nan.19. “Gama ta wurin Doka na mutu ga Doka saboda in rayu ga Allah.20. An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.21. Ba na ajiyar alherin Allah a gefe, gama da a ce ana samun adalci ta wurin Doka, ai, da Kiristi ya mutu a banza ke nan!” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.