Baibul a cikin shekara guda Satumba 25Ishaya 41:1-291. “Ku yi shiru a gabana, ku tsibirai! Bari al’ummai su sabunta ƙarfinsu! Bari su zo gaba su yi magana; bari mu sadu a wurin shari’a.2. “Wa ya zuga wannan daga gabas, yana kiransa cikin adalci ga yin hidima? Ya miƙa masa al’ummai ya kuma yi nasara da sarakuna a gabansa. Ya mai da su ƙura da takobinsa, zuwa inda iska ke hurawa ta wurin bugun da ya yi musu.3. Ya fafare su ya kuma yi tafiyarsa lafiya ƙalau, a hanyar da ƙafafunsa ba su taɓa bi ba.4. Wane ne ya taɓa yin haka ya kuma sa ya faru, yana kira ga tsararraki daga farko? Ni, Ubangiji ina can tun farkonsu ni kuma ina can har ƙarshe, Ni ne shi.”5. Tsibirai sun gan shi suka kuma ji tsoro; iyakokin duniya sun yi rawar jiki. Suka kusato suka kuma zo gaba;6. kowa na taimakon wani yana ce wa ɗan’uwansa, “Ka ƙarfafa!”7. Masassaƙi yakan ƙarfafa maƙerin zinariya, kuma shi mai gyara da guduma ya yi sumul yakan ƙarfafa mai harhaɗawa. Ya ce game da haɗin, “Ya yi kyau.” Yakan buga ƙusoshi su riƙe gunkin don kada yă fāɗi.8. “Amma kai, ya Isra’ila, bawana, Yaƙub, wanda na zaɓa, zuriyar Ibrahim abokina,9. na ɗauke ka daga iyakar duniya, daga kusurwoyi masu nesa na kira ka. Na ce, ‘Kai bawana ne’; na zaɓe ka ban kuwa ƙi ka ba.10. Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai; kada ka karai, gama ni ne Allahnka. Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka; zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.11. “Duk wanda ya yi fushi da kai tabbatacce zai sha kunya da ƙasƙanci; waɗanda suka yi hamayya da kai za su zama kamar ba kome ba su kuma hallaka.12. Ko ka nemi abokan gābanka, ba za ka same su ba. Waɗanda suke yaƙi da kai za su zama kamar ba kome ba.13. Gama ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya riƙe ka da hannun damana ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro; zan taimake ka.14. Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub marar ƙarfi, ya ƙaramin Isra’ila, gama ni kaina zan taimake ka,” in ji Ubangiji, Mai Fansarka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.15. “Duba, zan sa ka cikin abin sussuka, saboda kuma mai kaifi mai haƙora da yawa. Za ka yi sussukar duwatsu ka ragargaza su, ka kuma farfashe tuddai su zama kamar yayi.16. Za ka tankaɗe su, iska kuma ta kwashe su, guguwa kuma za tă warwatsa su. Amma za ka yi farin ciki a cikin Ubangiji ka kuma ɗaukaka a cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila.17. “Matalauta da mabukata suna neman ruwa, amma babu kome; harsunansu sun bushe saboda ƙishi. Amma Ni Ubangiji zan amsa musu; Ni, Allah na Isra’ila, ba zan yashe su ba.18. Zan sa koguna su malalo a ƙeƙasassun tuddai, maɓulɓulan ruwa kuma a kwaruruka. Zan mai da hamada tafkunan ruwa, busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓulɓulan ruwa.19. Zan sa a hamada ta tsiro da al’ul da itacen ƙirya, da itacen ci-zaƙi, da zaitun. Zan sa itace mai girma a ƙasashe masu sanyi ya tsiro a ƙeƙasasshiyar ƙasa, tare da fir da kuma saifires,20. don mutane su gani su kuma sani, su lura su kuma fahimci, cewa hannun Ubangiji ne ya aikata haka, cewa Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya sa abin ya faru.21. “Ka gabatar da damuwarka,” in ji Ubangiji. “Ka kawo gardandaminka,” in ji Sarki na Yaƙub.22. “Ka shigar da gumakanka don su faɗa mana abin da zai faru. Faɗa mana abubuwan da suka riga suka faru, domin mu lura da su mu kuma san abin da zai faru a ƙarshe. Ko kuwa ku furta mana abubuwan da za su faru,23. faɗa mana abin da nan gaba ta ƙunsa, don mu san cewa ku alloli ne. Ku yi wani abu, mai kyau ko mummuna, don mu ji tsoro da fargaba.24. Amma ku ba kome ba ne kuma ayyukanku banza da wofi ne; duk wanda ya zaɓe ku abin ƙyama ne.25. “Na zuga wani daga arewa, ya kuwa zo, wani daga inda rana ke fitowa wanda yake kira bisa sunana. Yana takawa a kan masu mulki kamar da taɓarya, sai ka ce maginin tukwane yana taka laka.26. Wa ya faɗi wannan tun daga farko, don mu sani, ko kafin ya faru, don mu ce, ‘Ya faɗi daidai’? Ba wanda ya faɗa wannan, ba wanda ya riga faɗe shi, ba wanda ya ji wata magana daga gare ku.27. Ni ne na farkon da ya ce wa Sihiyona, ‘Duba, ga su nan!’ Na ba wa Urushalima saƙon labari mai daɗi.28. Na duba amma ba kowa ba wani a cikinsu da zai ba da shawara, ba wani da zai ba da amsa sa’ad da na tambaye su.29. Duba, dukansu masu ƙarya ne! Ayyukansu ba su da riba; siffofinsu iska ne kawai da ruɗami.Ishaya 42:1-251. “Ga bawana, wanda na ɗaukaka, zaɓaɓɓen nan nawa wanda nake jin daɗi; Zan sa Ruhuna a cikinsa zai kuwa kawo adalci ga al’ummai.2. Ba zai yi ihu ko ya tā da murya, ko ya daga muryarsa a tituna ba.3. Iwan da ta tanƙware ba zai karye ba, ba zai kashe lagwani mai hayaƙi ba. Cikin aminci zai kawo adalci;4. ba zai kāsa ko ya karai ba sai ya kafa adalci a duniya. Cikin dokarsa tsibirai za su sa zuciya.”5. Ga abin da Allah Ubangiji ya ce, shi da ya halicci sammai ya kuma miƙe su, wanda ya shimfiɗa duniya da dukan abin da ya fito cikinta, wanda ya ba wa mutanenta numfashi, da rai ga waɗanda suke tafiya a kanta.6. “Ni Ubangiji, na kira ka cikin adalci; zan riƙe hannunka. Zan kiyaye ka in kuma sa ka zama alkawari ga mutane haske kuma ga Al’ummai,7. don ka buɗe idanun makafi ka ’yantar da kamammu daga kurkuku kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu.8. “Ni ne Ubangiji; sunana ke nan! Ba zan ba da ɗaukakata ga wani ba ko yabona ga gumaka.9. Duba, abubuwan da sun tabbata, sababbin abubuwa kuwa nake furtawa; kafin ma su soma faruwa na sanar da su gare ku.”10. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, ku yi yabonsa daga iyakar duniya, ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa, ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.11. Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu; bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki. Bari mutanen Sela su rera don farin ciki; bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu.12. Bari su ɗaukaka Ubangiji su kuma yi shelar yabonsa a tsibirai.13. Ubangiji zai fita ya yi yaƙi kamar mai ƙarfi, kamar jarumi zai yi himma; da ihu zai tā da kirarin yaƙi zai kuma yi nasara a kan abokan gābansa.14. “Na daɗe ina shiru, na yi shiru na kuma ƙame kaina. Amma yanzu, kamar mace mai naƙuda, na yi ƙara, ina nishi ina kuma haki.15. Zan lalatar da duwatsu da tuddai in busar da dukan itatuwansu; zan mai da koguna su zama tsibirai in kuma busar da tafkuna.16. Zan yi wa makafi jagora a hanyoyin da ba su taɓa sani ba, a hanyoyin da ba a saba ba zan bishe su; zan mai da duhu ya zama haske a gabansu in kuma mai da ƙasa mai kururrumai ta zama sumul. Abubuwan da zan yi ke nan; ba zan yashe su ba.17. Amma waɗanda suka dogara ga gumaka, waɗanda suke ce wa siffofi, ‘Ku ne allolinmu,’ za a mai da su baya da kunya.18. “Ka ji, kai kurma; duba, kai makaho, ka kuma gani!19. Wane ne makaho in ba bawana ba, da kuma kurma in ba ɗan aikan da na aika ba? Wane ne makaho kamar wanda ya miƙa kai gare ni, makaho kamar bawan Ubangiji?20. Kun ga abubuwa masu yawa, amma ba ku kula ba; kunnuwanku suna a buɗe, amma ba kwa jin wani abu.”21. Yakan gamsar da Ubangiji saboda adalcinsa ya sa dokarsa ta zama mai girma da kuma mai ɗaukaka.22. Amma ga mutanen da aka washe aka kuma kwashe ganima, an yi wa dukansu tarko a cikin rammuka ko kuma an ɓoye su cikin kurkuku. Sun zama ganima, babu wani da zai kuɓutar da su; an mai da su ganima, ba wanda zai ce, “Mayar da su.”23. Wane ne a cikinku zai saurari wannan ko ya kasa kunne sosai a cikin kwanaki masu zuwa?24. Wa ya ba da Yaƙub don yă zama ganima Isra’ila kuma ga masu kwasar ganima? Ba Ubangiji ba ne, wanda kuka yi wa zunubi? Gama ba su bi hanyoyinsa ba; ba su yi biyayya da dokarsa ba.25. Saboda haka ya zuba musu zafin fushinsa, yaƙi mai tsanani. Ya rufe su cikin harsunan wuta, duk da haka ba su gane ba; ya cinye su, amma ba su koyi kome ba.Zabura 109:26-3126. Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna; ka cece ni bisa ga ƙaunarka.27. Bari su san cewa hannunka ne, cewa kai ne, ya Ubangiji, ka yi shi.28. Za su iya la’anta, amma kai za ka sa albarka; sa’ad da suka tasar za su sha kunya, amma bawanka zai yi farin ciki.29. Masu zargina za su sha kunya za a rufe su da kunya kamar mayafi.30. Da bakina zan ɗaukaka Ubangiji sosai; cikin babban taro zan yabe shi.31. Gama yana tsaya a hannun damar mai bukata, don yă cece ransa daga waɗanda suke hukunta shi.Karin Magana 26:3-43. Bulala don doki, linzami don jaki, sanda kuma don bayan wawaye!4. Kada ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba kai kanka za ka zama kamar sa.Galatiyawa 3:1-291. Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ruɗe ku? A idanunku aka bayyana Yesu Kiristi gicciyeyye a sarari.2. Zan so in san abu guda tak daga gare ku. Kun karɓi Ruhu ta wurin kiyaye Doka ne, ko kuwa ta wurin gaskata abin da kuka ji?3. Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Bayan kun fara da Ruhu, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa?4. Ashe, wahaloli dabam-dabam da kuka sha sun zama a banza ke nan? Haka zai yiwu kuwa?5. Allah ya ba ku Ruhunsa yana kuma aikata ayyukan banmamaki a cikinku saboda kuna kiyaye Doka ne, ko kuwa domin kuna gaskatawa abin da kuka ji ne?6. Ku dubi Ibrahim mana, “Ya gaskata Allah, aka kuwa lissafta wannan adalci ne a gare shi.”7. Ku sani fa, waɗannan waɗanda suka gaskata, ’ya’yan Ibrahim ne.8. Nassi ya hanga cewa Allah zai kuɓutar da Al’ummai ta wurin bangaskiya, ya kuwa sanar wa Ibrahim wannan bisharar tun kafin lokaci yă yi cewa, “Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinka.”9. Saboda haka waɗanda suke da bangaskiya sun sami albarka tare da Ibrahim, mutumin bangaskiya.10. Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka la’anannu ne, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.”11. A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”12. Doka ba tă dangana ga bangaskiya ba; a maimakon haka, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”13. Kiristi ya fanshe mu daga la’anar Doka ta wurin zama la’ana saboda mu, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda aka rataye a kan itace.”14. Ya fanshe mu domin albarkar da aka yi wa Ibrahim yă zo ga Al’ummai, ta wurin Kiristi Yesu, domin ta wurin bangaskiya mu karɓi alkawarin Ruhu.15. ’Yan’uwa, bari in yi muku misali da rayuwarmu ta yau da kullum. Kamar dai yadda ba mai kawarwa ko yă ƙara wani abu cikin alkawarin da mutane suka kafa, haka yake a wannan batu.16. Alkawaran nan fa ga Ibrahim ne aka faɗa da kuma wani zuriyarsa. Nassi bai ce, “da zuriyoyi ba” wanda ya nuna kamar mutane da yawa, amma “ga zuriyarka,” wanda yake nufin mutum ɗaya, wanda shi ne Kiristi.17. Abin da nake nufi shi ne, Dokar da aka shigar ita bayan shekaru 430, ba tă kawar da alkawarin da Allah ya yi tun dā ba.18. Gama da a ce gādon yă dangana a kan doka ne, ai, da ba zai dangana a kan alkawari ba; amma Allah cikin alherinsa ya ba wa Ibrahim gādon ta wurin alkawari.19. To, don me aka kawo Doka? An yi ƙari da Doka ne don fitowa da laifi fili har kafin na zuriyan nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an ba da doka ta wurin mala’iku ne, aka kuma danƙa ta a hannun matsakanci.20. Kuma akan bukaci wani a tsakani ne idan da mutum biyu ake zance, Allah kuwa ɗaya ne.21. To, Dokar ce tana gāba da alkawaran Allah ke nan? Sam, ko kaɗan! Gama da a ce an ba da Dokar da tana iya ba da rai, tabbatacce, da sai a sami adalci ta wurin Doka.22. Amma Nassi ya kulle kome a ƙarƙashin ikon zunubi, domin abin da aka yi alkawarin nan, da ake bayar ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi, a ba da shi ga waɗanda suka gaskata.23. Kafin bangaskiyan nan tă zo, mun kasance a daure a kurkuku a ƙarƙashin Doka, a kulle sai da bangaskiyar da za tă zo ta bayyana.24. Ta haka aka sa Dokar ta zama jagorarmu zuwa ga Kiristi don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya.25. Yanzu da bangaskiya ta zo, ba sauran zamanmu a ƙarƙashin Doka.26. Dukanku ’ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.27. Gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi, kuna sanye da Kiristi ke nan.28. Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da ’yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu.29. In kuwa ku na Kiristi ne, to, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda kuma bisa ga alkawarin nan. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.