Baibul a cikin shekara guda Satumba 27Ishaya 45:1-251. “Ga abin da Ubangiji ya faɗa wa shafaffensa, ga Sairus, wanda hannun damansa yana riƙe da shi don yă ci al’ummai a gabansa ya kuma tuɓe makaman sarakuna, don yă buɗe ƙofofi a gabansa don kada a kulle ƙofofi.2. Zan sha gabanka in baje duwatsu; zan farfashe ƙofofin tagulla in kuma kakkarye ƙyamaren ƙarfe.3. Zan ba ka dukiyar duhu, arzikin da aka ajiye a asirtattun wurare, saboda ka san cewa ni ne Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya kira ka da suna.4. Saboda sunan Yaƙub bawana, Isra’ila zaɓaɓɓena, na kira ka da suna na ba ka matsayin bangirma, ko da yake ba ka san ni ba.5. Ni ne Ubangiji, kuma babu wani; in ban da ni babu wani Allah. Zan ƙarfafa ka, ko da yake ba ka san ni ba,6. saboda daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta mutane za su san cewa babu wani in ban da ni. Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.7. Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu, ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i; ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa.8. “Ku sammai, ku sauko da adalci kamar ruwan sama; bari gizagizai su zubar da yayyafi kamar adalci. Bari ƙasa ta buɗe, bari ceto ya tsiro, bari adalci ya yi girma tare da shi; ni, Ubangiji ne, na sa ya faru.9. “Kaitonka mai gardama da Wanda ya yi ka, da wanda yake kasko a cikin kasko a ƙasa. Yumɓu ya iya ce wa magini, ‘Me kake yi?’ Aikinka na iya cewa, ‘Ba shi da hannuwa’?10. Kaiton wanda yake cewa mahaifinsa, ‘Me ka manta?’ Ko kuwa ga mahaifiyarsa, ‘Me kin haifa?’11. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, da kuma Mahaliccinsa. Game da abubuwan da ke zuwa, kun tambaye ni game da ’ya’yana, ko kuwa kun ba ni umarni game da aikin hannuwana?12. Ai, ni ne wanda ya yi duniya na kuma halicci mutum a kanta. Hannuwana ne sun miƙe sammai; na umarci rundunar sararin sama.13. Zan tā da Sairus cikin adalcina. Zan sa dukan hanyoyinsa su miƙe. Zai sāke gina birnina ya kuma ’yantar da mutanena masu bautar talala, amma ba don wata haya ko lada ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.”14. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kayayyakin Masar da hajar Kush, da waɗannan dogayen Sabenawa, za su ƙetaro zuwa wurinku za su kuma zama naku; za su bi bayanku, suna zuwa cikin sarƙoƙi. Za su rusuna a gabanku su roƙe ku, suna cewa, ‘Tabbas Allah yana tare da ku, babu kuma wani; babu wani allah.’ ”15. Tabbatacce kai ne Allah wanda ya ɓoye kanka, Ya Allah da Mai Ceton Isra’ila.16. Dukan masu yin gumaka za su sha kunya; za su fita da kunya gaba ɗaya.17. Amma Ubangiji zai ceci Isra’ila da madawwamin ceto; ba za ku sāke shan kunya ko ƙasƙanci ba, har abada.18. Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicci sammai, shi ne Allah; shi da ya sarrafa ya kuma yi duniya, ya kafa ta; bai halicce ta don ta zama ba kome ba, amma ya yi ta don a zauna a ciki, ya ce, “Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.19. Ban yi magana asirce ba, daga wani wuri a ƙasar duhu ba; ban faɗa wa zuriyar Yaƙub, ‘Ku neme ni a banza ba.’ Ni, Ubangiji maganar gaskiya nake yi; na furta abin da yake daidai.20. “Ku tattaru ku zo; ku taru, ku masu gudun hijira daga al’ummai. Masu jahilci ne waɗanda suke ɗaukan gumakan katakai suna yawo, waɗanda suke addu’a ga allolin da ba za su cece su ba.21. Furta abin da zai kasance, ku gabatar da shi, bari su yi shawara tare. Wa ya faɗa wannan tuntuni, wa ya yi shelar sa a kwanakin dā? Ba ni ba ne, Ubangiji? Kuma babu Allah in ban da ni, Allah mai adalci da kuma Mai Ceto; babu wani sai ni.22. “Ku juyo gare ni ku sami ceto, dukanku iyakokin duniya; gama ni ne Allah, kuma babu wani.23. Da kaina na rantse, bakina ya furta cikin dukan mutunci kalmar da ba za a janye ba. A gabana kowace gwiwa za tă durƙusa; ta wurina kowane harshe zai rantse.24. Za su yi zance game da ni su ce, ‘A cikin Ubangiji kaɗai akwai adalci da kuma ƙarfafawa.’ ” Duk wanda ya yi fushi da shi zai zo wurinsa ya kuma sha kunya.25. Amma a cikin Ubangiji dukan zuriyar Isra’ila za su sami adalci za su kuwa yi yabo.Ishaya 46:1-131. Bel ya rusuna, Nebo ya durƙusa ƙasa; ana ɗaukan gumakansu a kan dabbobi ne. Siffofin da ake yawo da su nawaya ne, kayan nauyi masu gajiyarwa.2. Sun durƙusa suka kuma rusuna tare; ba su iya kuɓutar da nauyin kaya su kansu sukan tafi bauta.3. “Ku kasa kunne gare ni, ya ku gidan Yaƙub, dukanku waɗanda kuka rage na gidan Isra’ila, ku da na lura da ku tun da aka yi cikinku, na kuma riƙe ku tun haihuwarku.4. Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku. Na yi ku zan kuma riƙe ku; zan lura da ku in kuma kuɓutar da ku.5. “Da wa za ku kwatanta ni ko ku ɗauka daidai da ni? Da wa nake kama da har da za ku kwatanta ni?6. Waɗansu sukan zubar da zinariya daga jaka su kuma auna azurfa a ma’auni; sukan yi haya maƙerin zinariya don yă ƙera allah, su kuma rusuna su yi masa sujada.7. Sukan daga shi a kafaɗunsu su kuma ɗauke shi; sukan kafa shi a tsaye a wurinsa, a can kuwa zai tsaya. Daga wannan wuri ba zai iya gusawa ba. Ko da wani ya nemi taimakonsa, ba ya amsawa; ba zai iya cetonsa daga wahala ba.8. “Ku tuna da wannan, ku sa shi a zuciya, ku riƙe shi a zuciya, ku ’yan tawaye.9. Ku tuna da abubuwan da suka riga suka faru, waɗannan na tun dā; ni ne Allah, kuma babu wani; ni ne Allah kuma babu wani kamar ni.10. Nakan sanar da ƙarshe tun daga farko, daga fil azal, abin da yake zuwa nan gaba. Na ce nufina zai tabbata, kuma zan aikata dukan abin da na gan dama.11. Daga gabas na kira tsuntsun da yake farauta; daga can ƙasa mai nesa, wani mutumin da zai cika nufina. Abin da na riga na faɗa, shi zan sa ya faru; abin da na shirya, shi zan aikata.12. Ku kasa kunne, ku masu taurinkai, ku da kuke nesa da adalci.13. Ina kawo adalcina kusa, ba shi da nisa; kuma cetona ba zai jinkirta ba. Zan yi wa Sihiyona ceto, darajata ga Isra’ila.Zabura 111:1-61. Yabi Ubangiji. Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro.2. Ayyukan Ubangiji da girma suke; dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu.3. Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne, adalcinsa kuma zai dawwama har abada.4. Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa; Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma.5. Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa; yakan tuna da alkawarinsa har abada.6. Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa, yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai.Karin Magana 26:10-1010. Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa.Galatiyawa 5:1-261. Saboda ’yanci ne Kiristi ya ’yantar da mu. Sai ku tsaya daram, kada ku yarda ku sāke komawa ƙarƙashin nauyin bauta.2. Ku lura da kalmomina! Ni Bulus ina gaya muku cewa in kuka yarda aka yi muku kaciya, wannan ya nuna Kiristi ba shi da amfani a gare ku ba ko kaɗan.3. Haka kuma ina ƙara sanar wa kowane mutumin da ya yarda aka yi masa kaciya cewa dole yă kiyaye dukan Doka.4. Ku da kuke ƙoƙarin kuɓuta ta wurin Doka an raba ku da Kiristi ke nan; kuka kuma fāɗi daga alheri.5. Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu.6. Gama a cikin Kiristi Yesu, kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna.7. Kun yi tsere mai kyau a dā. Wa ya shige gabanku ya hana ku bin gaskiya?8. Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne.9. “Ɗan yisti kaɗan ne yake gama dukan curin burodi.”10. Ina da tabbaci cikin Ubangiji cewa ba za ku bi wani ra’ayi dabam ba. Wannan da yake rikita ku za a hukunta shi, ko shi wane ne.11. ’Yan’uwa, da a ce har yanzu ina wa’azin kaciya ne, to, me ya sa ake tsananta mini har yanzu? In haka ne, ashe, an kawar da abin da yake sa tuntuɓe game da gicciye ke nan.12. Da ma a ce masu tā da hankalinku ɗin nan su yanke gabansu gaba ɗaya mana!13. Ku ’yan’uwana, an kira ku ga zama ’yantattu. Amma kada ku yi amfani da ’yancinku don aikata ayyukan mutuntaka a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna.14. Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”15. In kun ci gaba da cizo, kuna kuma cin naman juna, ku yi hankali in ba haka ba za ku hallaka juna.16. Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka ba.17. Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa gāba suke da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so.18. Amma in Ruhu ne yake bishe ku, ba ku a ƙarƙashin Doka ke nan.19. Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata;20. bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya,21. da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.22. Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci,23. sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.24. Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma sha’awace-sha’awacensa.25. Da yake muna rayuwa ta Ruhu ne, bari mu ci gaba da al’amuranmu ta wurin Ruhu.26. Kada mu zama masu girman kai, muna tsokana muna kuma jin kishin juna. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.