Baibul a cikin shekara guda Satumba 30Ishaya 51:1-231. “Ku kasa kunne gare ni, ku da kuna neman adalci kuke kuma neman Ubangiji. Dubi dutse daga inda aka yanke ku da kuma mahaƙar duwatsu inda aka fafe ku;2. dubi Ibrahim, mahaifinku, da Saratu, wadda ta haife ku. Sa’ad da na kira shi kaɗai ne, na kuma albarkace shi na kuma mai da shi da yawa.3. Tabbatacce Ubangiji zai ta’azantar da Sihiyona zai kuma duba da tausayi a kan dukan kufanta; zai sa hamadanta ta zama kamar Eden, ƙeƙasasshiyar ƙasarta kamar lambun Ubangiji. Za a sami farin ciki da murna a cikinta, godiya da ƙarar rerawa.4. “Ku kasa kunne gare ni, mutanena; ku ji ni, al’ummata. Doka za tă fito daga gare ni; shari’ata za tă zama haske ga al’ummai.5. Adalcina na zuwa da sauri, cetona yana a kan hanya, hannuna kuma zai kawo adalci ga al’ummai. Tsibirai za su dube ni su kuma jira da sa zuciya don hannuna.6. Ku daga idanunku zuwa sammai ku dubi duniya a ƙasa; sammai za su ɓace kamar hayaƙi, duniya za tă shuɗe kamar riga mazaunanta kuma su mutu kamar ƙudaje. Amma cetona zai dawwama har abada, adalcina ba zai taɓa kāsa ba.7. “Ku ji ni, ku da kuka san abin da yake daidai, ku mutanen da kuke da dokata a zukatanku. Kada ku ji tsoron ba’ar da mutane suke yi ko ku firgita saboda zargin da suke yi.8. Gama asu za su cinye su kamar riga; tsutsotsi za su cinye su kamar ulu. Amma adalcina zai dawwama har abada, cetona har dukan zamanai.”9. Ka tashi, ka tashi! Ka yafa wa kanka ƙarfi, Ya hannun Ubangiji; ka farka, kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a zamanai na dā. Ba kai ba ne wanda ya yayyanka Rahab gunduwa-gunduwa, wanda ya soki dodon ruwan nan?10. Ba kai ba ne ka busar da teku, ka busar da ruwan zurfafa masu girma, wanda ya yi hanya a cikin zurfafan teku saboda fansassu su ƙetare?11. Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo. Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi; madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani. Murna da farin ciki zai cika su, baƙin ciki da nishi zai ɓace.12. “Ni kaɗai ne na ta’azantar da ku. Wane ne ku da kuke tsoron mutane masu mutuwa, ’ya’yan mutane waɗanda suke ciyawa ne kawai,13. har da kuka manta da Ubangiji Mahaliccinku, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya, har kuna zama da tsoro kowace rana saboda fushin masu zalunci, waɗanda sun ƙudura sai sun hallaka? Gama ina fushin mai zalunci?14. Ba da daɗewa za a ’yantar da ’yan kurkuku; ba za su mutu a kurkuku ba, ba kuwa za su rasa abinci ba.15. Gama ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya dama teku domin raƙumansa su yi ruri, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.16. Na sa maganata a bakinka na kuma rufe ka da inuwar hannuna, Na shimfiɗa sammai, na kafa harsashen duniya, na kuma ce wa Sihiyona, ‘Ku mutanena ne.’ ”17. Ki farka, ki farka! Ki tashi, ya Urushalima, ke da kika sha daga hannun Ubangiji kwaf na fushinsa, ke da kika shanye har ƙasar kwaf kwaf da ya sa mutane suna tangaɗi.18. Cikin dukan ’ya’yan da ta haifa; cikin dukan ’ya’yan da ta yi reno babu wani da zai kama hannunta.19. Waɗannan masifu riɓi biyu sun auko miki, wa zai ta’azantar da ke? Lalaci da hallaka, yunwa da takobi, wa zai ƙarfafa ki?20. ’Ya’yanki sun sume; sun kwanta kusurwar kowane titi, kamar barewar da aka kama da tarko. Sun cika da fushin Ubangiji da kuma tsawatawar Allahnki.21. Saboda haka ki ji wannan, ke mai wahala, wadda ta bugu, amma ba da ruwan inabi.22. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, Allahnki, wanda ya kāre mutanensa, “Duba, na ƙwace daga hannunki kwaf da ya sa ki tangaɗi; daga wannan kwaf, kwaf na fushina, ba za ki ƙara sha ba.23. Zan sa shi a hannuwan masu gwada miki azaba, waɗanda suke ce miki, ‘Fāɗi rubda ciki don mu iya taka a kanki.’ Kika kuma mai da bayanki kamar ƙasa, kamar titin da ake takawa a kai.”Ishaya 52:1-151. Ki farka, ki farka, ya Sihiyona, ki sanya wa kanki ƙarfi. Ki sa rigarki na daraja, Ya Urushalima, birni mai tsarki. Marasa kaciya da maƙazanta ba za su shi cikinki ba.2. Ki kakkaɓe ƙurarki; ki tashi, ki zauna a kursiyinki, ya Urushalima. Ki ’yantar da kanki daga sarƙoƙi a wuyanki, Ke kamammiyar Diyar Sihiyona.3. Gama ga abin Ubangiji yana cewa, “An sayar da ke ba da kuɗi ba, kuma ba da kuɗi za a fanshe ki ba.”4. Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Da farko mutanena suka gangara zuwa Masar don su zauna; a baya-bayan nan, Assuriya sun zalunce su.5. “Yanzu kuma me nake da shi a nan?” In ji Ubangiji. “Gama an kwashe mutanena ba a bakin kome ba kuma waɗanda suka mallake su sun yi musu ba’a, Kullum ana cin gaba da yin wa sunana saɓo.6. Saboda haka mutanena za su san sunana; saboda haka a wannan rana za su san cewa ni ne wanda ya faɗa wannan. I, ni ne.”7. Me ya fi wannan kyau a kan duwatsu a ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗi waɗanda suke shelar salama, waɗanda suke kawo labari mai daɗi, waɗanda suke shelar ceto, waɗanda suke ce wa Sihiyona, “Allahnki yana mulki!”8. Ki kasa kunne! Masu tsaronki sun tā da muryoyinsu; tare sun yi sowa ta farin ciki. Sa’ad da Ubangiji ya komo Sihiyona, za su gan shi da idanunsu.9. Ku ɓarke cikin waƙoƙin farin ciki gaba ɗaya, kangonki na Urushalima, gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa, ya fanshi Urushalima.10. Ubangiji zai nuna hannunsa mai tsarki a fili a idanun dukan al’ummai, da kuma dukan iyakokin duniya za su gani ceton Allahnmu.11. Ku fita, ku fita daga can! Kada ku taɓa wani abu marar tsarki! Ku fita daga cikinta ku zama da tsarki, ku da kuke ɗaukan kayan aikin Ubangiji.12. Amma ba za ku fita a gaggauce ba ko ku tafi da gudu; gama Ubangiji zai ja gabanku, Allah na Isra’ila zai kasance mai tsaron bayanku.13. Duba, bawana zai aikata abubuwa da hikima; za a tā da shi a kuma ɗaga shi da ɗaukaka ƙwarai.14. Kamar dai yadda aka kasance da mutane masu yawa waɗanda suka giggice sa’ad da suka gan shi, kamanninsa ya lalace ƙwarai fiye da na kowane mutum siffarsa kuma ta yi muni fiye da yadda ta mutum take,15. haka zai ba al’ummai masu yawa mamaki, sarakuna kuma za su riƙe bakunansu don mamaki. Gama abin da ba a faɗa musu ba, shi za su gani, kuma abin da ba su ji ba, shi za su fahimta.Zabura 112:5-105. Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake, shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.6. Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba; za a tuna da mai adalci har abada.7. Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba; zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.8. Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba; a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa.9. Ya rarraba kyautansa ga matalauta, adalcinsa zai dawwama har abada; za a ɗaga ƙahonsa sama da bangirma.10. Mugun mutum zai gani yă kuma yi fushi, zai ciza haƙora yă kuma lalace; sha’awace-sha’awacen mugaye za su zo ga ƙarshe.Karin Magana 26:16-1616. Rago yana gani yana da hikima fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu.Afisawa 2:1-221. Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku.2. Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah.3. Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah.4. Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai,5. ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku.6. Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya.7. Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu.8. Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah.9. Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai.10. Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.11. Saboda haka, ku tuna dā ku Al’ummai ne bisa ga haihuwa, waɗanda kuma ake kira masu “kaciya” sukan kira ku “marasa kaciya” (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu).12. Ku kuma tuna a lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Isra’ila, ba ku kuma da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah.13. Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi.14. Gama shi kansa shi ne salamarmu, shi ne ya kawo ƙungiyoyi biyu suka zama ɗaya, ya kuma rushe katangan nan ta ƙiyayya wadda ta raba mu.15. Kiristi ya ba da jikinsa don yă kawar da doka da dukan umarnanta da kuma ƙa’idodinta. Ya yi haka domin yă halicci sabuwar zuriya daga zuriyoyin nan biyu. Ta haka kuma ya kawo salama tsakaninsu.16. A kan gicciye, Kiristi ya kawar da ƙiyayyar da take tsakaninmu da juna. Ya kuma kawo sulhu tsakaninmu da Allah.17. Ya zo ya yi muku wa’azin salama; ku da kuke nesa da shi, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa.18. Gama ta wurinsa dukanmu za mu iya zuwa gun Uba ta wurin Ruhu guda.19. Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma.20. Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci na ginin.21. Ta wurinsa ne dukan ginin yake a haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi girma, yă zama haikali mai tsarki domin Ubangiji.22. Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.