Baibul a cikin shekara guda Satumba 4Waƙar Waƙoƙi 7:1-131. Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne, Ya diyar sarki! Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja, aikin hannun gwanin sassaƙa.2. Cibinki kamar kwaf ne da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba. Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama wanda furen bi-rana ya kewaye.3. Nonanki sun yi kamar bareyi biyu, tagwayen barewa.4. Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa. Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon kusa da ƙofar Bat Rabbim. Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon wadda take duban Damaskus.5. Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel. Gashinki ya yi kamar shunayya; yakan ɗauke hankalin sarki.6. Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi, Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo!7. Tsayinki ya yi kamar itacen dabino, kuma nonanki sun yi kamar ’ya’yan itace.8. Na ce, “Zan hau itacen dabino; zan kama ’ya’yansa.” Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa, ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa,9. kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau. Bari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena, yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora.10. Ni ta ƙaunataccena ce, kuma sha’awarsa domina ne.11. Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari, bari mu kwana a ƙauye.12. Bari mu tafi gonar inabi da sassafe don mu ga ko kuringar ta yi ’ya’ya, ko furanninsu sun buɗe, ko rumman sun yi fure, a can zan nuna maka ƙaunata.13. Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu, a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi, sabo da tsoho, da na ajiye dominka, ƙaunataccena.Waƙar Waƙoƙi 8:1-141. Da a ce kai ɗan’uwa ne gare ni, wanda nonon mahaifiyata sun shayar! Da in na same ka a waje, na sumbace ka, babu wanda zai rena ni.2. Da sai in bi da kai in kawo ka gidan mahaifiyata, ita da ta koyar da ni. Da na ba ka ruwan inabi gaurayayye da kayan yaji ka sha, zaƙin rumman nawa.3. Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina, hannunsa na dama kuma ya rungume ni.4. ’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle.5. Wace ce wannan da take haurawa daga hamada tana dogara a kan ƙaunataccenta? A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke, a wurin da aka haife ki, wurin da mahaifiyarki ta haife ki.6. Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka, kamar hatimi a hannunka; gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa, kishinta yana kamar muguntar kabari, yana ƙuna kamar wuta mai ci, kamar gagarumar wuta.7. Ruwa da yawa ba zai iya kashe ƙauna ba, koguna ba za su iya kwashe ta ba. In wani zai bayar da dukan dukiyar gidansa don ƙauna, za a yi masa dariya ne kawai.8. Muna da ƙanuwa, nonanta ba su riga sun yi girma ba. Me za mu yi da ƙanuwarmu a ranar da za a yi maganar sonta?9. Da a ce ita katanga ce, da sai mu gina hasumiyar azurfa a kanta. Da a ce ita ƙofa ce, da sai mun yi mata ƙyauren itacen al’ul.10. Ni katanga ce kuma nonaina sun yi kamar hasumiya. Ta haka na zama idanunsa kamar wanda yake kawo gamsuwa.11. Solomon ya kasance da gonar inabi a Ba’al-Hamon; ya ba da hayar gonar inabi ga ’yan haya. Kowanne zai biya shekel dubu na azurfa don ’ya’yan inabin.12. Amma gonar inabina nawa ne da zan bayar; shekel dubu naka ne, ya Solomon, kuma ɗari biyu na waɗanda suke lura da ’ya’yan itatuwansa ne.13. Ke da kike zaune a cikin lambu da ƙawaye suna lura da ke, bari in ji muryarki!14. Ka zo, ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko kuwa kamar ’yar batsiya a kan dutsen da kayan yaji suke a shimfiɗe.Zabura 104:31-3531. Bari ɗaukakar Ubangiji ta dawwama har abada; bari Ubangiji yă yi farin ciki cikin aikinsa,32. shi wanda ya dubi duniya, sai ta razana, wanda ya taɓa duwatsu, sai suka yi hayaƙi.33. Zan rera ga Ubangiji dukan raina; zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.34. Bari tunanina yă gamshe shi, yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji.35. Amma bari masu zunubi su ɓace daga duniya mugaye kuma kada a ƙara ganinsu. Yabi Ubangiji, ya raina. Yabi Ubangiji.Karin Magana 24:21-2221. Ka ji tsoron Ubangiji da kuma sarki, ɗana, kuma kada ka haɗa kai da masu tayarwa,22. gama za a tura waɗannan biyu zuwa hallaka nan da nan, kuma wa ya sani irin bala’in da za su iya kawowa?1 Korintiyawa 14:1-201. Ku bi halin ƙauna kuna kuma marmarin neman baye-bayen ruhaniya, musamman baiwar annabci.2. Gama duk wanda yake magana da wani harshe ba da mutane yake magana ba, sai dai da Allah. Tabbatacce, ba wanda yake fahimtarsa; yana faɗin asirai ta wurin ruhu ne.3. Amma duk wanda yake annabci, yana magana ne da mutane domin yă gina su, yă ƙarfafa su, yă kuma yi musu ta’aziyya.4. Wanda yake magana da wani harshe kuwa, kansa yake gina, amma mai annabci, ikkilisiya ce yake gina.5. Zan so kowannenku yă yi magana da harsuna, sai dai zan fi so ku yi annabci. Wanda yake annabci ya fi wanda yake magana da harsuna, sai dai in ya fassara don ikkilisiya ta ginu.6. To, ’yan’uwa, a ce na zo wurinku ina kuma yin magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani ko sani ko annabci, ko kuma kalmar koyarwa ba?7. Abubuwan nan marasa rai ma da sukan yi ƙara, kamar su algaita ko molo, in muryarsu ba tă fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa?8. Haka ma in ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi?9. Haka yake sa’ad da kuka yi magana da waɗansu harsunan da ba a fahimta. In babu wanda zai san abin da kuke faɗi, za ka dai yi wa iska magana ne kawai.10. Ba shakka akwai harsuna iri-iri a duniya, duk da haka kowane a cikinsu yana da ma’ana.11. To, in ban gane ma’anar abin da wani yake faɗi ba, ni baƙo ne ga mai maganar, shi kuma baƙo ne a gare ni.12. Haka yake a gare ku. Da yake kuna marmarin samun baye-bayen ruhaniya, sai ku ba da ƙarfinku ga yin amfani da waɗanda za su gina ikkilisiya.13. Saboda haka, duk wanda yake magana da harshe, sai yă yi addu’a a yi masa baiwar fassara.14. Gama in na yi addu’a da wani harshe, ruhuna ne yake addu’a, amma tunanina bai amfana kome ba.15. To, me zan yi? Akwai lokutan da zan yi addu’a da ruhuna; akwai kuma lokutan da zan yi addu’a da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina.16. A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, sa’ad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba?17. Ko da yake kuna ba da godiya da kyau, amma wancan mutumin da yake tare da ku bai ginu ba.18. Na gode wa Allah, domin ina magana da harsuna fiye da ku duka.19. Amma a cikin ikkilisiya zan gwammace in yi magana da kalmomi biyar da za a fahimta don in koyar da waɗansu da a ce in yi magana da kalmomi guda dubu goma a wani harshe.20. ’Yan’uwa, ku daina tunani kamar yara. Wajen mugunta ku zama jarirai, sai dai wajen tunaninku, ku zama manya. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.