Baibul a cikin shekara guda Satumba 8Ishaya 7:1-251. Sa’ad da Ahaz ɗan Yotam, ɗan Uzziya, yake sarkin Yahuda, Sarki Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su yaƙi Urushalima, amma ba su iya cinta da yaƙi ba.2. Sai fa aka faɗa wa gidan Dawuda cewa, “Aram ya haɗa kansa da Efraim”; saboda haka zuciyar Ahaz da ta mutanensa suka firgita, sai ka ce itatuwa a kurmin da iska ta girgiza.3. Sai Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Fita, kai da ɗanka Sheyar-Yashub, don ku sadu da Ahaz a ƙarshen wuriyar da take kawo ruwa daga Tafkin Tudu, a hanyar Filin Mai Wanki.4. Ka faɗa masa, ‘Ka yi hankali, ka natsu kada kuma ka ji tsoro ko ka damu, kada ka ji tsoron fushin sarki Rezin da na Aram da na ɗan Remaliya, ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin ’yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba.5. Aram, Efraim da ɗan Remaliya sun ƙulla maƙarƙashiya, suna cewa,6. “Bari mu kai wa Yahuda hari; bari mu yayyage su mu rarraba su a tsakaninmu, mu naɗa Tabeyel sarki a kansu.”7. Duk da haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “ ‘Ba zai faru ba, ba zai auku ba,8. gama kan Aram shi ne Damaskus, kan Damaskus kuma kawai shi ne Rezin. Cikin shekaru sittin da biyar za a wargaje Efraim har ba za tă iya rayuwa ta zama al’umma ba.9. Kan Efraim shi ne Samariya, kan Samariya kuma kawai shi ne ɗan Remaliya. In ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiyarku ba, ba za ku dawwama ba.’ ”10. Ubangiji ya kuma yi magana wa Ahaz ya ce,11. “Ka roƙi Ubangiji Allahnka yă ba ka alama, ko daga zurfafa masu zurfi ko kuwa daga can cikin sama.”12. Amma Ahaz ya ce, “Ba zan nema ba; ba zan gwada Ubangiji ba.”13. Sa’an nan Ishaya ya ce, “To, ku saurara, ya ku gidan Dawuda! Abin kirki kuke yi ne da kuka ƙure haƙurin jama’a? Ko haƙurin Allah ne kuma kuke so ku ƙure?14. Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, za tă kuwa kira shi Immanuwel.15. In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa.16. Amma kafin yaron yă isa yanke shawara yă ƙi abin da yake mummuna, yă zaɓi abin da yake nagari, ƙasashen sarakunan nan biyu da kuke tsoro za su zama kango.17. Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama’arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Efraim daga na Yahuda, zai kawo sarkin Assuriya.”18. A wannan rana Ubangiji zai yi feɗuwa yă kira ƙudaje daga rafuffuka masu nisa na Masar da kuma ƙudan zuma daga ƙasar Assuriya.19. Za su zo su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, a kan dukan ƙayayyuwa da dukan rammukan ruwa.20. A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da rezan da aka yi haya daga ƙetaren Kogi, sarkin Assuriya ke nan, yă aske kanku da gashin ƙafafunku, zai kuma aske gemunku.21. A ranar, mutum zai bar karsana ɗaya da awaki biyu da rai.22. Kuma saboda yalwa madarar da suke bayarwa, zai kasance da madarar da zai sha. Dukan waɗanda suka rage a ƙasar za su sha madara da zuma.23. A wannan rana, a kowane wuri inda akwai kuringa dubu da kuɗinsu ya kai shekel dubu na azurfa, ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne kawai za su kasance a can.24. Mutane za su je can da baka da kibiyoyi, gama ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne za su rufe ƙasar.25. Game da dukan tuddai da dā ake nome da garemani kuwa, ba za ku ƙara je wurin ba saboda tsoron ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya; za su zama wuraren da ake kai shanu a sake su su yi ta yawo da kansu, tumaki kuma su yi ta gudu.Ishaya 8:1-221. Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki naɗaɗɗen littafi mai girma ka yi rubutu a kai da alƙalami kurum, Maher-Shalal-Hash-Baz.2. Zan kuma kira Uriya firist da Zakariya ɗan Yeberekiya su zama mini amintattun shaidu.”3. Sa’an nan na tafi na yi jima’i da annabiya, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa. Ubangiji kuma ya ce mini, “Raɗa masa suna, Maher-Shalal-Hash-Baz.4. Kafin yaron yă san yadda zai ce ‘Babana’ ko ‘Mamana,’ sarkin Assuriya zai kwashe arzikin Damaskus da ganimar Samariya.”5. Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce,6. “Domin wannan jama’a ta ƙi natsattsen ruwan rafin Shilowa suka yi ta farin ciki a kan Rezin ɗan Remaliya,7. saboda haka Ubangiji yana shirin yă kawo musu rigyawar ruwan Kogi, wato, sarkin Assuriya da dukan sojojinsa. Zai cika dukan gaɓoɓinsa, yă kuma malala har zuwa bakin kogi.8. Yă yi ta malala har zuwa cikin Yahuda, yă shafe ta, yana ratsa ta ciki har yă kai kafaɗa. Fikafikansa da ya buɗe za su rufe fāɗin ƙasarka, Ya Immanuwel!”9. Ku yi kururuwar yaƙi, ku ƙasashe, ku kuma ji tsoro! Ku saurara, dukanku manisantan ƙasashe. Ku shirya don yaƙi, ku kuma ji tsoro!10. Ku ƙirƙiro dabarunku, amma ba za su yi nasara ba; ku ƙulla shirye-shiryenku, amma ba za su yi amfani ba, gama Allah yana tare da mu.11. Ubangiji ya yi mini magana da hannunsa mai ƙarfi a kaina, yana yi mini gargaɗi kada in bi hanyar waɗannan mutane. Ya ce,12. “Kada ka kira wani abu makirci game da kome da waɗannan mutane suke kira makirci; kada ji tsoron abin da suke tsoro, kada kuma ka firgita game da shi.13. Ubangiji Maɗaukaki shi ne za ka ɗauka a matsayi mai tsarki, shi ne wanda za ka ji tsoro, shi ne za ka yi rawar jiki a gabansa,14. zai kuwa kasance a wuri mai tsarki; amma ga dukan gidajen Isra’ila zai zama dutsen da zai sa mutane su yi tuntuɓe dutse kuma da zai sa su fāɗi. Ga dukan mutanen Urushalima kuma zai zama tarko da raga.15. Yawancinsu za su yi tuntuɓe; za su fāɗi a kuwa ragargaza su, za a sa musu tarko a kuma kama su.”16. Ɗaura shaidar nan ta gargadi ka kuma yimƙe umarnin Allah a cikin almajiraina.17. Zan saurari Ubangiji, wanda ya ɓoye fuskarsa daga gidan Yaƙub. Zan dogara gare shi.18. Ga ni, da yaran da Ubangiji ya ba ni. Mu alamu ne da shaidu a cikin Isra’ila daga Ubangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a Dutsen Sihiyona.19. Sa’ad da mutane suka ce muku ku nemi shawarar ’yan bori da masu sihiri, waɗanda suke shaƙe murya har ba a jin abin da suke faɗi, bai kamata mutane su nemi shawara daga Allahnsu ba? Me zai sa ku nemi shawara daga matattu a madadin masu rai?20. Nemi umarnin Allah da kuma shaidar jan kunne. Duk wanda bai yi magana bisa ga wannan kalma ba, ba su da amfani.21. Cikin matsuwa da yunwa, za su yi ta kai komo ko’ina a ƙasar; sa’ad da suka ji yunwa, za su yi fushi su tā da idanu sama, su zagi sarkinsu da Allahnsu.22. Sa’an nan za su zura wa ƙasa idanu, abin da za su gani kawai shi ne matsuwa da duhu da kuma abin banrazana, za a kuma jefa su cikin baƙin duhu.Zabura 105:37-4537. Ya fitar da Isra’ila, ɗauke da azurfa da zinariya, kuma daga cikin kabilansu babu wani da ya kāsa.38. Masar ta yi murna sa’ad da suka tafi, saboda tsoron Isra’ila ya fāɗo musu.39. Ya shimfiɗa girgije kamar mayafi, da kuma wuta don ta ba su haske da dare.40. Suka roƙa, ya kuwa ba su makware ya kuma ƙosar da su da abinci daga sama.41. Ya buɗe dutse, sai ruwa ya ɓulɓulo, kamar kogi ya gudu zuwa cikin hamada.42. Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki da ya ba wa bawansa Ibrahim.43. Ya fitar da mutanensa da farin ciki, zaɓaɓɓunsa da sowa ta farin ciki;44. ya ba su ƙasashen al’ummai, suka kuma sami gādon abin da waɗansu sun sha wahala a kai,45. don su kiyaye farillansa su kuma kiyaye dokokinsa. Yabo ga Ubangiji.Karin Magana 24:30-3430. Na wuce cikin gonar rago, na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci;31. ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina, ciyayi sun rufe ƙasar, katangar duwatsu duk ta rushe.32. Na yi tunani a zuciyata na kuwa koyi darasi daga abin da na gani.33. Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,34. sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.1 Korintiyawa 16:1-241. To, game da tara kuɗi domin taimakon mutanen Allah, ku yi abin da na gaya wa ikkilisiyoyin Galatiyawa.2. A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba.3. In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima.4. In kuma ya dace in tafi, to, sai su tafi tare da ni.5. Bayan na zazzaga Makidoniya, zan zo wurinku, domin zan ratsa ta Makidoniya.6. Wataƙila zan ɗan jima a wajenku, ko ma in ci damina a can, domin ku yi mini rakiya a tafiyata, duk inda za ni.7. Ba na so in gan ku yanzu in wuce kawai, ina fata zan yi ’yan kwanaki tare da ku, in Ubangiji ya yarda.8. Sai dai zan kasance a Afisa har lokacin Fentekos,9. domin an buɗe mini wata hanya mai fāɗi don aiki mai amfani, ko da yake akwai mutane da yawa masu gāba da ni.10. In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.11. Kada fa wani yă ƙi karɓansa. Ku sallame shi lafiya, domin yă koma wurina. Ina duban hanyarsa tare da ’yan’uwa.12. Batun ɗan’uwanmu Afollos kuwa, na roƙe shi sosai yă zo wurinku tare da ’yan’uwa. Bai so zuwa yanzu ba, amma zai zo in ya sami zarafi.13. Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.14. Ku yi kome da ƙauna.15. Kun san cewa iyalin gidan Istifanas ne suka fara tuba a Akayya. Sun kuma ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima. Ina roƙonku ’yan’uwa,16. ku ba da kanku ga irin waɗannan, ga kuma kowa da ya haɗa hannu a aikin, yana kuma faman a cikinsa.17. Na yi farin ciki da isowar Istifanas, Fortunatus da Akaikus, domin sun biya bukatar da ba ku iya biya ba.18. Gama sun wartsake ruhuna da kuma naku. Ya kamata ku girmama irin waɗannan mutane.19. Ikkilisiyoyin da suke a lardin Asiya suna gaisuwa. Akwila da Firiskila suna gaishe ku sosai cikin Ubangiji, haka ma ikkilisiyar da takan taru a gidansu.20. Dukan ’yan’uwa a nan suna gaisuwa. Ku gai da juna da sumba mai tsarki.21. Ni, Bulus nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna.22. Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji, la’ana ta zauna a kansa. Zo, ya Ubangiji!23. Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da ku.24. Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙaunata cikin Kiristi Yesu. Amin. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.