Ayoyin Baibul Akan Maudu'i

Batutuwa
Allah
Hali Mai Kyau
Muguwar Hali
Zunubai
Rayuwa
Coci
Abubuwa
Mala'iku da Aljannu
Alamomin lissafi
Arin
Allah: [Albarka]
Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.”
Masu albarka ne waɗanda suke makoki, gama za a yi musu ta’aziyya.
Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.
Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.
[24] “ ‘ “ Ubangiji yă albarkace ku, yă kuma kiyaye ku; [25] Ubangiji yă sa fuskarsa ta haskaka a kanku, yă kuma yi muku alheri;
[6] Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. [7] Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
[7] “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji, wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji. [8] Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi. Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo; ganyayensa kullum kore suke. Ba shi da damuwa a shekarar fări ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”
Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai; kada ka karai, gama ni ne Allahnka. Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka; zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
Daga yalwar alherinsa dukanmu muka sami albarka bisa albarka.
[16] ya ce, “Na rantse da kaina, in ji Ubangiji, domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba, [17] tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu,
[28] Allah yă ba ka daga raɓar sama da kuma yalwar ƙasa, yalwar hatsi da sabon ruwan inabi. [29] Bari al’ummai su bauta maka mutane kuma su rusuna maka. Ka zama shugaba a kan ’yan’uwanka bari kuma ’ya’yan mahaifiyarka su rusuna maka. Bari waɗanda suka la’anta ka, su la’antu; waɗanda kuma suka sa maka albarka, su sami albarka.”
[1] Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a. [2] Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana. [3] Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.
[1] Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba, [2] Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa, yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya, [3] yakan maido da raina. Yakan bi da ni a hanyoyin adalci saboda sunansa. [4] Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya.
[3] Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona. Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona. Daga mutane masu fitina, ka cece ni. [4] “Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa tsira daga abokan gābana.
Mun san cewa kowane haifaffe na Allah ba ya cin gaba da yin zunubi; kasancewarsa haifaffe na Allah ita takan kāre shi, mugun kuwa ba zai iya cuce shi ba.
Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala, kana kiyaye raina; ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana, da hannunka na dama ka cece ni.
Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.
Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
Hausa Bible 2020
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ 2009, 2020 by Biblica, Inc.